An ga Georgina Rodriguez dauke da kayan adon fam £775, 000

An ga Georgina Rodriguez dauke da kayan adon fam £775, 000

Ba sabon labari ba ne cewa Cristiano Ronaldo ya na cikin manyan ‘yan kwallon da aka taba gani a Duniya. Bayan haka, Tauraron Duniyar ba karamin Attajiri ba ne.

A dalilin ficen da Cristiano Ronaldo ya yi, kusan ko ina ya je akwai idanun jama’a a kansa. Har Iyalinsa da dangi da na kusa da shi ba su tsira daga idon Duniya ba.

Kwanan nan labarin kyakkyawar Budurwarsa watau Miss Georgina Rodriguez, ya sake shiga gari bayan da aka gan ta dauke da wani abin hannu mai ‘dan-karen tsada.

Georgina Rodriguez ta sanya wani awarwaron zinari ne wanda kudinsa ya kai fam 775, 000 na kudin Euro. Jaridar The Sun ta kasar Ingila ce ta fitar da wannan rahoto.

KU KARANTA: Matar Cristiano Ronaldo zai aura ta haifa masa jaririya

A kudin Najeriya a halin yanzu idan aka yi lissafi, wannan awarwaron zinari da Budurwar Tauraron na kungiyar Juventus ta ke dauke da shi ya zarce miliyan 270.

Miss Georgina Rodriguez ba ta fito daga babban gida ba, ta ma hadu da Ronaldo ne a wani shago a lokacin da ake biyanta Euro 250 duk mako a matsayin yarinyar shago.

Kafin Georgina Rodriguez wanda haifaffar wani Kauye a kasar Sifen ce ta hadu da Ronaldo, abin da ta ke samu a wajen sana’ar ta bai wuce N10, 000 a kudin Najeiya ba.

A halin yanzu duk wata Ronaldo ya kan ba Mahaifiyar ‘Diyarsa Naira miliyan 32. Watakila wannan ya bata damar sayen awarwaron zinari na dalar Euro 775, 000.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel