Shugaban FIFA Ya Yi Magana kan Buga Gasar Cin Kofin Duniya a Najeriya

Shugaban FIFA Ya Yi Magana kan Buga Gasar Cin Kofin Duniya a Najeriya

  • Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya ce a halin yanzu Najeriya ba ta shirya karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya ba
  • Infantino ya ce Najeriya na buƙatar zuba jari a filayen wasa, otal-otal, filayen jiragen sama da hanyoyin sufuri kafin ta iya karɓar babbar gasar
  • Sai dai ya bayyana cewa Najeriya tana da arziki, sha’awar ƙwallon ƙafa da kuma ƙudurin da ake buƙata domin karɓar gasar a nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya bayyana cewa Najeriya ba ta shirya karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya a halin yanzu ba, saboda akwai buƙatar inganta muhimman abubuwan more rayuwa.

Infantino ya bayyana hakan ne a wata hira yayin da yake amsa tambaya kan abubuwan da ake buƙata domin ƙasa irin Najeriya ta karɓi baƙuncin gasar.

Kara karanta wannan

Matawalle ya raba motoci 1000 za su shiga lunguna nemawa Tinubu kuri'u

Gianni Infantino
Shugaban FIFA, Gianni Infantino. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Arise News ta wallafa cewa shugaban FIFA ya ce ababen more rayuwa su ne ginshiƙin shirya gasar, musamman filayen wasa, otal-otal, filayen jiragen sama da hanyoyin sufuri.

Maganar Gianni Infantino kan Najeriya

Da aka tambaye shi kai tsaye ko Najeriya ta shirya karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya, Infantino ya amsa da cewa a yanzu ba ta shirya ba, amma hakan na iya yiwuwa a nan gaba.

Ya ce Najeriya tana da albarkatun ƙasa, sha’awa da kuma ƙudurin da ake buƙata, amma dole ne a zuba jari sosai a fannin ababen more rayuwa.

Najeriya ta karɓi baƙuncin gasar FIFA ta ƙarshe ne a shekarar 2009, lokacin da ta shirya gasar cin kofin duniya ta ’yan ƙasa da shekara 17.

A wasan ƙarshe na gasar, Switzerland ta doke Golden Eaglets ta Najeriya da ci 1-0 a Abuja kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Infantino ya yaba wa FIFA

Da yake magana kan shekaru 10 da ya yi a matsayin shugaban FIFA, Infantino ya ce ci gaban hukumar da faɗaɗa gasar ƙwallon ƙafa sun nuna irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancinsa.

Kara karanta wannan

Shugaban FIFA ya leƙo ayyukan alherin Tinubu, ya faɗi ɓangaren da ya yi fice

Ya bayyana cewa kuɗin shigar FIFA sun ƙaru daga sama da dala biliyan 5 kafin ya zama shugaban hukumar zuwa dala biliyan 16 a zagayen gasar da ya gabata.

Kofin duniya
Kofin duniya a filin wasa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce ƙwallon ƙafa da FIFA na ci gaba da bunƙasa, amma hakan na buƙatar aiki tuƙuru da bin ƙa’idoji mafi inganci.

Infantino ya ziyarci Najeriya a ƙarshen makon da ya gabata, inda a ranar Juma’a ya duba sabon fasalin filin wasa na Warri tare da babban sakataren FIFA, Mattias Grafström.

Ronaldo ya yi ritaya a Portugal

A wani labarin, kun ji cewa shahararren ɗan ƙwallon ƙafa Cristiano Ronaldo ya sanar da shirin yin ritaya daga buga wa tawagar ƙasar Portugal wasa.

Ya buga wa Portugal wasanni 234, inda ya zura ƙwallaye 146, abin da ya sa ya zama ɗan wasan da ya fi kowa yawan wasanni da ƙwallaye a tarihin tawagar ƙasar.

Ɗan wasan da ke taka leda a ƙungiyar Al-Nassr ta Saudiyya ya jagoranci Portugal ta lashe gasar Euro 2016 da kuma gasar UEFA Nations League ta 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng