Sabon Dan Wasa, Suleiman Mubarak zai Fara Kwallo a Super Eagles ta Najeriya

Sabon Dan Wasa, Suleiman Mubarak zai Fara Kwallo a Super Eagles ta Najeriya

  • Suleiman Mubarak mai shekara 19 ya samu gayyata zuwa tawagar Super Eagles bayan bajintar da yake yi a kungiyar Slavia Prague ta Jamhuriyar Czech
  • Matashin dan wasan tsakiya ya fara taka leda a Right2Win Academy da ke Abuja kafin ya koma Slavia Prague a shekarar 2025
  • Rahoto ya nuna cewa Mubarak ya ci kwallaye biyar tare da bayar da taimakon kwallo uku a wasanni 13 da ya buga a dukkan gasanni a bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Matashin dan wasan Najeriya, Suleiman Mubarak, na daga cikin sababbin ’yan wasa da suka samu gayyata zuwa tawagar Super Eagles bayan bajintar da ya nuna a kungiyar Slavia Prague, zakarun gasar Jamhuriyar Czech.

Dan wasan mai shekara 19 ya samu damar shiga tawagar babbar kungiyar ne bayan ya burge masu horaswa a matakan matasa da kuma tawagar ’yan wasan kungiyar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba kowace 'yar wasa a tawagar Flamingos kyautar Naira miliyan 100

Suleiman Mubarak
Suleiman Mubarak da ya samu gayyata zuwa Super Eagles. Hoto: Sports N9a
Source: Facebook

Yadda Mubarak ya fara taka leda

Punch ta wallafa cewa Mubarak ya fara nuna bajintarsa ne a Right2Win Academy da ke Abuja, kafin ya koma kungiyar Slavia Prague a shekarar 2025.

A kungiyar matasa ta Slavia Prague, ya yi fice musamman a gasar UEFA Youth League, inda ya zura kwallaye biyar a wasanni shida da ya buga da wasu manyan makarantun kwallon kafa na Turai.

Wannan bajinta ta ba shi damar buga wa tawagar ajiyar kungiyar wasa a gasar Czech National Football League, kafin daga bisani aka daga shi zuwa babbar tawagar a farkon shekarar 2026.

A ranar 7 ga Fabrairu, 2026, Mubarak ya fara buga wasansa na farko a babbar tawagar Slavia Prague, inda ya ci kwallo a wasan da kungiyar ta doke Mladá Boleslav da ci 4-0.

Sports Nigeria ta wallafa cewa ya shigo wasan ne a mintunan karshe, amma ya samu damar zura kwallo ta hudu, inda ya fara nuna irin gudunmawar da zai iya bayarwa ga kungiyar.

Kara karanta wannan

Bayan faɗuwar ɗanyen mai a duniya, FCCPC ta waiwayo kan farashin fetur a Najeriya

Bajintarsa ta taimaka wa Slavia

Mubarak ya ci gaba da samun damar buga wa babbar kungiyar wasa, wadda ta lashe kofin gasar Czech First League ta kakar 2025/2026. Wannan shi ne karo na tara da Slavia Prague ta lashe kofin gasar.

A watan Satumban 2026, kungiyar ta saka masa hannu kan sabon kwantiragi da zai ci gaba da zama a cikinta har zuwa ranar 30 ga Yunin 2031.

A bana, dan wasan ya ci kwallaye uku tare da taimakawa wajen samar da wasu kwallaye uku a wasanni tara na gasar firimiyar Czech.

Haka kuma, ya ci kwallaye biyu a gasar cin kofin Czech, wanda ya kai adadinsa zuwa kwallaye biyar da taimakon kwallo uku a wasanni 13 da ya buga a dukkan gasanni.

Daga cikin wasannin akwai guda uku da ya buga a gasar zakarun Turai ta UEFA Champions League.

A ranar Lahadi, Mubarak ya taimaka wajen samar da kwallon farko da dan wasan Czech, Mojmír Chytil, ya ci a wasan da Slavia Prague ta doke Artis Brno da ci 4-1.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa zai yi wahala 'yan adawa su iya kayar da Bola Tinubu a zaɓen 2027"

Mubarak ya kafa tarihi a Turai

A ranar 20 ga Oktoba, Mubarak ya fara wasa a karawar da Slavia Prague ta tashi 2-2 da Fenerbahçe a gasar UEFA Champions League, inda ya shafe mintuna 85 a filin wasa.

Wannan ya sanya shi zama dan Najeriya mafi karancin shekaru da ya fara buga wasan gasar zakarun Turai tun bayan da Alex Iwobi ya yi hakan a Arsenal a karawar da ta yi da Barcelona a watan Maris na 2016.

Rahotanni sun nuna cewa kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya fara tunanin gayyatar Mubarak ne zuwa tawagar ’yan kasa da shekara 23, wadda ke shirin buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta matasa ta 2027.

Sai dai bayan rahotannin da ’yan leken asirin kocin suka gabatar kan bajintar matashin, musamman a gasar zakarun Turai, sai aka mika masa gayyata zuwa babbar tawagar Super Eagles.

Suleiman Mubarak na taka leda
Suleiman Mubarak a filin wasa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Matashin ya isa sansanin Super Eagles a ranar Laraba domin shirin wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2027 da Tanzania.

Kara karanta wannan

Sarakunan Yarbawa a jihohin Arewa 19 sun dauki babban alkawari ga Tinubu

Daga bisani ya shiga atisaye tare da sauran ’yan wasan tawagar, yayin da tawagar ta kammala cika adadinta gabanin wasan farko da za a yi ranar Juma’a a Uyo.

Najeriya ta lashe kofin duniya

A wani labarin, mun ruwaito cewa tawagar matan Najeriya ta kasa da shekara 17 ta lashe gasar cin kofin duniya ta FIFA U-17 ta 2026 bayan ta doke Japan da ci 2-1 a wasan karshe.

Wannan nasara ta zama karon farko da Najeriya ta lashe kofin duniya a wannan matakin na mata, sannan ta zama kasa ta farko daga nahiyar Afirka da ta dauki kofin.

A wasan karshe da Japan, ’yan matan Najeriya sun nuna jajircewa, inda suka samu nasara da ci 2-1 bayan fafatawa mai zafi a farkon wasan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng