Senegal Vs Morocco: CAS Ta Yanke Hukuncin Karshe kan Wanda Ya Lashe Gasar Cin Kofin Afirka

Senegal Vs Morocco: CAS Ta Yanke Hukuncin Karshe kan Wanda Ya Lashe Gasar Cin Kofin Afirka

  • Kotun sasanta rikicin wasanni (CAS) ta soke hukuncin Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) na ƙwace wa Senegal kofin AFCON na 2025
  • Hukuncin da aka yanke ranar Talata, 24 ga Nuwamba, 2026, ya tabbatar da nasarar Senegal ta 1-0 a wasan ƙarshe da aka buga a Rabat
  • Senegal ta kai ƙara CAS ne bayan kwamitin ɗaukaka ƙara na CAF ya ce ta yi rashin nasara a wasan saboda ’yan wasanta sun bar fili

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Senegal -;Kotun sasanta rikicin wasanni (CAS) ta soke hukuncin da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta yanke na ƙwace wa Senegal kofin gasar cin kofin ƙasashen Afirka (AFCON) ta 2025 tare da bai wa Morocco.

Kotun CAS ta tabbstar da Senegal a matsayin ta lashe gasar cin kofin AFCON na 2025 tare da maida mata da kambun gasar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe malamai 2, sun yi awon gaba da mutane sama da 10

Daily Trust ta ce Hukuncin da kotun ta yanke ranar Talata, 24 ga Nuwamba, 2026, ya tabbatar da nasarar da Senegal ta samu da ci 1-0 a kan Morocco mai masaukin baki a wasan ƙarshe da aka buga a Rabat ranar 18 ga Janairu.

Hakan ya kawo ƙarshen watanni na rashin tabbas kan ƙasar da ta kamata ta mallaki kofin na bara.

Da farko dai an ayyana Senegal a matsayin zakara bayan ta doke Morocco a karin lokacin wasa, sakamakon ƙwallon da Pape Gueye ya ci.

Sai dai daga baya kwamitin ɗaukaka ƙara na CAF ya soke wannan sakamakon, inda ya bayyana cewa Senegal ta yi rashin nasara a wasan bayan ’yan wasanta sun bar fili saboda rashin amincewa da bugun fenaritin da aka bai wa Morocco.

CAF ta sanar da hukuncin ranar 17 ga Maris, inda ta ba Morocco nasara da ci 3-0 tare da kofin AFCON. Wannan mataki ya sa Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal (FSF) ta garzaya ta daukaka kara zuwa CAS.

Senegal ta yi iƙirarin cewa alkalin wasa ya amince a ci gaba da fafatawa bayan ’yan wasan sun dawo filin wasa, don haka ya kamata a tabbatar da sakamakon da aka samu a wasan.

Kara karanta wannan

Rashin Imani: Yan bindiga sun rutsa bayin Allah suna barci, sun bude masu wuta

Abin da ya haddasa rikicin

Rikicin ya samo asali ne daga abin da ya faru a mintunan ƙarshe na lokacin wasa 90, lokacin da alkalin wasa ɗan ƙasar Kongo, Jean-Jacques Ndala, ya bai wa Morocco bugun fenariti bayan nazarin bidiyon taimakon alƙalai (VAR).

Zanga-zangar ’yan wasan Senegal ta jawo tsaikon kusan mintuna 15. Wasu daga cikinsu sun nufi ɗakin sauya kaya kafin kyaftin ɗin tawagar, Sadio Mané, ya lallashe su suka dawo filin.

Bayan an ci gaba da wasan, Brahim Diaz na Morocco ya kasa cin bugun fenaritin. Mai tsaron ragar Senegal, Edouard Mendy, ya tare bugun da ya yi irin na Panenka.

Daga nan aka tafi karin lokaci, inda Pape Gueye ya ci ƙwallon da ta ba Senegal nasara tare da kofin gasar.

Sai dai kwamitin ɗaukaka ƙara na CAF ya soke sakamakon, bisa dogaro da sashe na 82 da na 84 na dokokin gasar AFCON. Waɗannan sassa sun tanadi hukunci ga ƙungiyar da ta ƙi buga wasa ko ta bar fili ba tare da izinin alkalin wasa ba.

A ranar 25 ga Maris, 2026, Senegal ta shigar da ƙara a CAS, tana ƙalubalantar hukuncin CAF tare da neman kotun ta dawo mata da matsayin zakara, wanda a halin yanzu ta smu nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262