Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo na shirin yin aure
– Babban Dan wasan nan Ronaldo na shirin yin aure
– Ronaldo zai auri Budurwar sa Georgina Rodriguez
– A shekara mai zuwa ne ‘Dan wasan zai zama Ango
Ana dai sa rai babban Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ya shiga daga ciki a badi kamar yadda labari yake zuwa mana.
Tauraron Dan wasan na Real Madrid Cristiano Ronaldo zai auri budurwar sa Georgina Rodriguez a shekara mai zuwa ko da dai har yau ba a san takamamen ranar ba. Yanzu haka dai Rodriguez mai shekaru 23 ta na da cikin ‘dan Ronaldo.
KU KARANTA: An kama wasu da ke yaudarar mata a Turai
Jaridar Correio de Manha tace Dan wasan dai ya ba Budurwar ta sa zobe mai tsada har na fam miliyan Euro £232,000 wanda ya kai kusan Naira Miliyan 100. Kwanan nan ne aka ga Rodriguez ta shiga Makarantar koyon rawa a Sifen.
Ronaldo ya samu jarirai tagwaye masu suna Mateo da Eve kwanakin baya, haka kuma dama dai yana da yaro mai shekaru 6 a Duniya. Ko da yake dai har yanzu Dan wasan bai tabbatar da ainihin iyayen yaran ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Tsakanin Arsenal da Chelsea su wa su ka fi 'Yan wasa?
Asali: Legit.ng