Siyasar Najeriya
Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wasu mutum uku sun gurfana a gaban kotu bisa zarginsu da aikata zamba, ciki har da kakakin majalisar jihar Ondo a Kudu.
Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi hasashen yadda zata iya kayawa a Kotu tsakanin mai gidansa da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Jam'iyyar Hope Democratic Party (HDP), ta shigar da sabuwar ƙara a gaban kotun ɗaukaka ƙara tana neman a hana rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa.
Yayin da ake tunkarar babban zaben gwamna a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, jam'iyyar APC mai mulkk ya samu gagarumin goyon baya ranar Talata.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum da takwaransa na jihar Yobe, Mai Mala Buni, ne a sahun gaba a kokarin ɗarewa kujerar shugaban kungiyar gwamnoni ta ƙasa.
Kungiyar mutanen yankin tsakiyar Najeriya, Middle Belt Forum ta ce abu guda da Shugaba Buhari zai yi idan yana son yafiya shine gyara kura-kuren da INEC ta yi.
Sanata Sani Musa ya yi fatali da rahotannin cewa ya janye daga takarar neman kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10. Sanatan ya ce har yanzu yana takara.
Zababben shugaban ƙasa a Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce lafiyarsa sumul kalau kuma ya shirya tsaf domin karban sikiyarin mulkin Najeriya a Mayu.
Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya roki talakawa su dubi girman Allah, su yafe masa kura-kuran da ya yi musu yana sane ko kuma bai sani ba a mulkinsa.
Siyasar Najeriya
Samu kari