"Cikin Sauƙi Zan Sa Tinubu Shan Kaye a Zaɓe Mai Zuwa" Cewar Atiku

"Cikin Sauƙi Zan Sa Tinubu Shan Kaye a Zaɓe Mai Zuwa" Cewar Atiku

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yafi ƙarfin abokin takarar sa na jam'iyyar APC
  • Alhaji Atiku Abubakar yayi nuni da cewa ko sau nawa za a fafata zaɓe, to tabbas sai yayi nasara akan Tinubu
  • Atikun ya bayyana haka ne ta hannun kwamitin yaƙin neman zaɓen sa, inda ya fasa ƙwai kan wani shiri da jam'iyyar APC ke yi

Abuja- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya cika baki cewa koda an ɗaga zaɓe sai ya kayar da abokin takarar sa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Rahoton Guardian

Atiku
Atiku na tattaunawa da Tinubu Hoto: Bola Tinubu
Asali: Facebook

Wannan iƙirarin na ƙunshe ne a wata takarda da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Atiku/Okowa ya fitar inda ya shawarci takwaran sa na ɓangaren Tinubu/Shettima da daina zawarcin ganin an ɗage zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Saura Kwana 3 Zabe, Kamfen Tinubu Ya Samu Tagomashin Manyan Fastoci 100

An shirya gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Kwamitin yaƙin neman zaɓen na Atiku-Okowa yace mafi yawan yan Najeriya sun yi watsi da ƙoƙarin da tsagin Tinubu suke yi domin ganin an ɗaga zaɓen. Rahoton Vanguard

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata sanarwa da kakakin kwamitin, Kola Ologbondiyan, ya fitar, ya bayyana cewa:

“Neman ganin an ɗaga zaɓe da kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima, ke yi wani shiri na ƙara kawo ruɗani da ɓata harkar zaɓe a ƙasar nan."

Kwamitin ya kuma tunatar da takwaran sa na tsagin Tinubu yadda wani babban gwamna a Arewa maso Yamma, ya sha kunya a zaman majalisar zartawa ta ƙasa na ƙarshe, inda yayi ƙoƙarin shigar da kuɗirin a ɗage zaɓen na wasu ƴan makonni.

"Muna da masaniya cewa wanann gwamnan yana son a ɗaga zaben ne saboda ɗan takarar jam'iyyar APC, Tinubu, baya da wata hanyar lashe zaɓe saboda yadda ƴan Najeriya suka ƙi aminta da shi."

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Hamshaƙan Attajirai 6 Dake Takara a Zaɓen 2023

“Abin takaici shine bayan rashin nasarar su a taron majalisar zartarwa, sun cigaba da yawo a kafafen sada zumunta suna neman a ɗage zaɓen." A cewar Ologbondiyan.

Ana Dab Da Zaɓe, Wasu Malaman Addini Sun Koma Bayan Tinubu

A wani labarin na daban kuma, kamfen ɗin Tinubu ya samo tagomashi, wasu malaman addini sun nuna goyon bayan su ga ɗan takarar.

Saura kwanaki uku kacal a fafata zaɓen shugaban ƙasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel