Kotun Daukaka Kara Ta Kori Dan Takarar Gwamnan PDP Na Jihar Akwa Ibom

Kotun Daukaka Kara Ta Kori Dan Takarar Gwamnan PDP Na Jihar Akwa Ibom

  • Kotun daukaka kara ya kori dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP saboda lura da wasu dalilai masu karfi
  • Wannan na zuwa ne bayan da a baya kotun tarayya ya ba PDP rashin gaskiya tare da tabbatar da dan takarar a matsayin sahihi
  • Ba wannan ne karon farko da ake korar dan takarar wata kujera ba a Najeriya, an sha yin hakan a baya

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara mai zama a Abuja a ranar Talata da yamma ya cire dan majalisar wakilai Hon. Micheal Enyong a matsayin dan takarar gwamnan APC a jihar Akwa Ibom.

A madadinsa, kotun ya maida Mr. Umo Eno, tsohon kwamishina a jihar, wanda babban kotun tarayya ya kora a ranar 20 ga watan Janairun 2023 gaskiya.

A hukuncin da ya yanke wanda PDP ta shigar don kalubalantar hukuncin kotun tarayya, mai shari’a Hamma Akawu Barka na kotun daukaka karan ya rushe hukuncin baya.

Kara karanta wannan

Rikici: Saura kwana 6 zabe, an harbe jigon APC a wurin taron kamfen a wata jihar PDP

An kori dan takarar gwamnan jihar Akwa Ibom na PDP
Kotun Daukaka Kara Ta Kori Dan Takarar Gwamnan PDP Na Jihar Akwa Ibom | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ba a yi gaskiya a kotun tarayya ba

A cewarsa, an samu kura-kurai a hukuncin da kotun tarayya ya yanke, kamar yadda jarida Tribune Online ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai shari’a Barka ya gamsu da hujjojin lauyoyin PDP, Mr Paul Usoro (SAN) da Uwemedimo Nwoko (SAN) da ke kan matsayar cewa kotun tarayya ya yi kuskure a hukuncinsa.

Hakazalika, ya gamsu da batunsu cewa, kotun tarayyan ya yi kuskuren fahimtar hujjojin mai shigar da kara a tun farko, don haka ya yi hukuncin da bai nuna adalci ba.

Dan takarar da aka kora zai biya N1m ga PDP

Kotun na daukaka kara ya kuma bayana cewa, batun da ke da alaka da deliget-deliget na zaben fidda gwanin da aka gudanar lamari ne na cikin gida, inda yace kotun daukaka kara bai yi duba ga wannan ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kotu Ta Yanke Sirikin Obasanjo Daurin Shekaru 7 A Gidan Yari

Har ila yau, mai shari’a ya gamsu da batun da Usoro ya gabatar cewa, kwamitin ayyukan jam’iyyar ne kadai ke da ikon gudanar zaben fidda gwani don zabo dan takarar babban zabe.

A gefe guda, kotun na daukaka kara ya ba dan majalisar umarnin ya biya N1m ga wadanda suka jam’iyyar PDP a matsayin kudin shigar da kara, rahoton Daily Post.

Da yake martani ga hukuncin, Usoro ya ce, kotun ya yi adalci kan hukuncin da kotun tarayya ya yanke kan PDP.

An yi shari’a mai kama da wannan, inda aka kori dan takarar gwamnan jihar Taraba bayan shiga kotu sau uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel