2023: Ku Yi Zaben Tumun Dare Ku Koma Cikin Duhu – Shehu Sani Ya Gargadi Yan Najeriya

2023: Ku Yi Zaben Tumun Dare Ku Koma Cikin Duhu – Shehu Sani Ya Gargadi Yan Najeriya

  • Tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani ya aika sako mai muhimmanci ga yan Najeriya musamman matasa
  • Gabannin zaben shugaban kasa na ranar Asabar, dan siyasan ya bukaci yan Najeriya da kada su zabi dan takara saboda malamai sun ce su zabe su
  • Sanatan ya bukaci masu zabe da su yi aiki da hankali a zabe mai zuwa domin zaben tumun dare zai sake jefa kasar a wahalar shekaru hudu

Dan siyasa kuma mai raddin kare hakkin dan adam, Shehu Sani ya aika sako ga yan Najeriya gabannin zaben shugaban kasa na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

A wata sanarwa da ya saki a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 21 ga watan Fabrairu, tsohon dan majalisar na Kaduna ya bukaci matasa da su yanke shawara mai kyau a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Saura kiris zabe, Limaman Katolika sun fadi wadanda za su zaba a zaben bana

Shehu Sani
2023: Ku Yi Zaben Tumin Dare Ku Koma Cikin Duhu – Shehu Sani Ya Gargadi Yan Najeriya Hoto: Senator Shehu Sani
Asali: Facebook

Ya ce kada su yarda ra'ayin shugabannin addini ya yi aiki sama da abun da zuciyarsu ke so wajen zaben wadanda za su jagorance su.

Ku yi zabe da hankali, Shehu Sani ga yan Najeriya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya wallafa a shafin nasa:

"A ranar Asabar wannan kasar tana da rana mai dauke da tarihi. Kada ku zabi dan takara saboda masallatai da cocinanku sun bukaci ku yi haka. Ku bi zuciyarku da gogewarku sannan ku zabi shugaba da ya cancanta. Zaben tumun dare zai zama tafiyar wasu shekaru hudu a duhu.

Jama'a sun yi martani

@b_usman06 ya yi martani:

"Yallabai ai basu gyara maka ba dasuka kada kai tun primary wlh."

@Arderm__kabo ya ce:

"Kwana biyu kwamared na maganan Hankali wlh.mungode yallabai."

@Harunas59526351 ya ce:

"Allah ya taimake mu."

@oyinbrakime

"Ka yi gaskiya yallabai."

@JideOyedokun ya ce:

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu ko Obi: Tsohon Dan Majalisa, Shehu Sani Ya Bayyana Yadda Ya Kamata A Samar Da Magajin Buhari

"Zan zabi duk wanda fasto na ya ce na zaba."

@EAPREZI ya ce:

"Ba mu yarda da cocinanmu da masallatanmu ba kuma. Za mu je zaben mai yiwuwa."

A wani labari na daban, tsohon karamin ministan shari'a kuma jigon PDP, Musa Elayo ya yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsu ne zai lashe zabe.

Elayo ya ce Atiku Abubakar da PDP za su kwato yankin arewa ta tsakiya wacce tun dama chan mallakin jam'iyyarsu ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel