Jam'iyyar PDP Ta Kori Dan Takarar Gwamna a Jigar Akwa Ibom

Jam'iyyar PDP Ta Kori Dan Takarar Gwamna a Jigar Akwa Ibom

  • Ana dab da zaben shugaban ƙasa, jam'iyyar PDP ta kori ɗan takarar gwamnan Akwa Ibom a zaben watan Maris mai zuwa
  • Tun bayan kammala zaben fidda gwani a shekarar 2022 ake tirka-tirka kan tikitin takarar gwamnan jihar
  • A ranar Jumu'a da ta shige aka ga INEC ta sauya ɗan takarar PDP a Akwa Ibom bayan umarnin Kotu

Akwa Ibom - Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Akwa Ibom ta fatattaki Michael Enyong, ɗan takarar gwamnan jihar a zaben da ke tafe.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa PDP mai mulkin jihar ta ɗauki wannan mataki ne kan zargin da ake masa na amfani da takardun Bogi.

Michael Enyong.
Jam'iyyar PDP Ta Kori Dan Takarar Gwamna a Jigar Akwa Ibom Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

Hakan na ƙunshe a wata wasika mai kwanan watan 30 ga watan Janairu kuma ɗauke da sa hannun shugaban PDP na ƙaramar hukumar Uyo, Anthony Eko, da mambobin majalisar zartaswa 14.

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Ekiti

Wasikar na ɗauke da adireshin shugaban PDP na jihar Akwa Ibom. Wanda abun ya shafa, Mista Enyong, mamban majalisar wakilan tarayya mai ci, ya fito ne daga Uyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan siyasan mai kimanin shekaru 54 a duniya, shi ne mamba mai wakiltar mazaɓar Uyo a majalisar wakilan tarayya kuma yana kan zango na biyu yanzu haka.

A ranar Jumu'a da ta shige, hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta wallafa sunan Enyong a matsayin sabon ɗan takarar gwamnan PDP a jihar.

Ya maye gurbin wanda gwamna Udom Emmmanuel ya zabi ya gaje shi, Umo Uno, kuma wanda ya lashe zaben fidda gwanin da PDP ta gudanar bara.

INEC ta ayyana, "Umarnin Kotu,' a matsayin dalilin da ya sa ta sauya ɗan takarar a shafinta na yanar gizo, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Wannan Cin Mutunci Ne" Gwamna Wike Ya Ƙara Fusata, Ya Yi Wa Atiku Tatas Ana Saura Kwana 5 Zabe

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa jam'iyyar PDP ta garzaya Kotun ɗaukaka ƙara domin dawo da tikitin takara hannun Mista Eno.

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Nasarar Oyebanji a Zaben Gwamnan Ekiti

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Ekiti ya sake nasara a Kotun ɗaukaka kara a ƙarar da aka shigar mai kalubalantar zabensa

Mista Oni, ɗan takarar gwamna a inuwar SDP ne ya kalubalanci sakamakon zaben wanda ya gudana ranar 18 ga watan Yuni, 2022.

Amma a zaman Kotun ɗaukaka kara na yau Talata ta fatattaki ƙarar bisa hujjar rashin cancanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel