Shugaban Kasa a 2023: Atiku Zai Lashe Zabe a Arewa Ta Tsakiya, Inji Tsohon Minista

Shugaban Kasa a 2023: Atiku Zai Lashe Zabe a Arewa Ta Tsakiya, Inji Tsohon Minista

  • Wani tsohon minista ya nuna kwarin gwiwa cewa dan takarar PDP, Atiku Abubakar, zai lashe babban kaso a arewa maso gabas
  • Yan kwanaki kafin zaben shugaban kasa, Musa Elayo, ya tabbatar da cewar Atiku zai yi gagarumin nasara a yankin saboda goyon bayan da yake da shi
  • Elayo ya bayyana cewa arewa ta tsakiya ta PDP ce kuma jam'iyyar ta shirya kwato ta a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu

Tsohon karamin ministan shari'a kuma mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Musa Elayo, ya nuna yakinin cewa dan takararsu zai lashe zabe a arewa ta tsakiya, rahoton Leadership.

Gabannin babban zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu, masu nazari kan harkokin zabe sun bayyana arewa ta tsakiya a matsayin filin daga ga manyan yan takarar babban kujera ta daya a kasar.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Manyan Malaman Addini Da Ke Takara a Zabe Mai Zuwa

Atiku ABubakar
Shugaban Kasa a 2023: Atiku Zai Lashe Zabe a Arewa Ta Tsakiya, Inji Tsohon Minista Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Tsohon minista ya bayyana yankin da Atiku zai lashe

A yanzu haka, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ce ke iko a jihohin yankin baya ga Benue, inda Samuel Ortom na PDP ke a matsayin gwamna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, Elayo wanda shine jagoran jam'iyyar a yankin ya ce a al'adance, arewa ta tsakiya mallakin PDP ne kuma za su kwato sa a ranar Asabar.

A wata hira da ya yi da jaridar Leadership a garin Lafiya, jihar Nasarawa, a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu, Elayo ya ce:

"Saboda haka, ina hango haske ga PDP a jihohin arewa ta tsakiya a wannan zaben mai zuwa."

Ina nan a PDP ba zan koma APC ba, Gwamna Wike

A wani labari na daban, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana cewa yana nan daram dam a PDP cewa karya ne baya shirin komawa APC kamar yadda ake ta hasashe.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe: PDP Ta Hadu Da Gagarumin Cikas a Kano, Tsagin Shehu Sagagi Sun Yi Maja Da Jam’iyyar Kwankwaso

Da yake magana a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu, Wike ya ce shakka babu halin dattako na jam'iyyar APC ya matukar burge shi domin sun tsaya tsayin daka a kan mulkin karba-karba.

A cewarsa gwamnonin jam'iyyar mai mulki sun jajirce sai da aka mika tikitin shugaban kasa ga yankin kudu kamar yadda suka yi yarjejeniya tun daga farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng