Karya Ce Ban Janyewa Atiku Takara Ba, Al-Mustapha Ya Magantu

Karya Ce Ban Janyewa Atiku Takara Ba, Al-Mustapha Ya Magantu

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Action Alliance (AA) ya fito fili ya ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa a kansa
  • Hamza Al-Mustapha wanda shine ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen ranar Asabar mai zuwa yace har yanzu yana nan kan bakansa na yin takara
  • Ɗan takarar ya kuma bayyana cewa komai rintsi ba zai taɓa janyewa wani ɗaɓ takara na daban ba

Abuja- Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa na jam'iyyar Action Alliance (AA), Maj. Hamza Al-Mustapha mai ritaya, yace koda wasa bai taɓa janyewa ko marawa takarar Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, baya ba.

Za dai a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya ranar Asabar mai zuwa.

Al-Mustapha ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da yayi da wani gidan rediyo a ranar Talata. Rahoton Vanguard

Kara karanta wannan

Ana Saura Kwana 3 Zaɓe, Atiku Ya Sha Wani Babban Alwashi Kan Tinubu

Al-Mustapha
Al-Mustapha Ya Magantu Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa tsantsar ƙarya ce raɗe-raɗen da ake yaɗawa cewa ya janyewa Atiku Abubakar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana sanarwar da ta fito daga ɓangaren tsagin shugabancin jam'iyyar na Kenneth Udeze, wanda a tanan ya samu takarar shugaban ƙasa, a matsayin zamba ce.

Sanarwar da wani mutum (Udeze) ya fitar cewa Action Alliance na goyon bayan Atiku, zamba ce.

"Action Alliance bata marawa kowa baya ba. Har yanzu ina cikin takara sannan idan zan faɗi, zan faɗi ne da kyau sannan zan yi nasara, zan yi nasara mai kyau." A cewar sa

Al-Mustapha, wanda shine ɗan takarar jam'iyyar AA da INEC ta san da zaman sa, yace har yanzu bai tattauna da kowa ba kan janye takara ko marawa wani ɗan takara baya. Rahoton PM News

Ya roƙi ƴan Najeriya da suyi watsi da wannan furucin da shugaban jam'iyyar yayi.

Kara karanta wannan

Saura Kwana 3 Zabe, Kamfen Tinubu Ya Samu Tagomashin Manyan Fastoci 100

Jam'iyyar dai a yanzu haka a rabe take gida biyu, inda take da ƴan takarar shugaban ƙasa har guda biyu.

Na Ga Peter Obi Yana Kuka: Cewar Fasto Daniels Yayin da Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben 2023

A wani labarin na daban kuma, wani fasto ya bayyana hasashen sa na wanda zai lashe zaɓen shugaban ƙasa.

Faston yace ya hango wani ɗan takara na sharɓar kuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel