Sake Fasalin Naira Zai Fi Cutar Da ’Yan Siyasa Fiye da Talakawan Najeriya, Inji Sarki Khalifa Sanusi

Sake Fasalin Naira Zai Fi Cutar Da ’Yan Siyasa Fiye da Talakawan Najeriya, Inji Sarki Khalifa Sanusi

  • Sarkin Kano Sanusi ya bayyana alherin sauyin kudi da aka yi a Najeriya, ya ce talaka ne zai mora nan kusa
  • A cewarsa, hakan zai rage murdiyar zabe da almundaha a lokutan zaben shugabanni da kasar za ta yi a mako mai zuwa
  • Ya kuma bayyana cewa, sauyin kudi zai fi cutar da ‘yan siyasa fiye da talakawan da ke neman na abinci a kasar

Legas - Sarkin Kano na 14 kuma tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Sarki Muhammadu Sanusi ya yi kira ga ‘yan Najeriiya da goyi bayan sabuwar dokar kudi ta CBN.

A wani rubutu da ya yada a kafar sada zumunta a ranar Litinin, Sanusi ya ce mutane su kula kada su fada tarkon yaudara na ‘yan siyasar kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Magana a Kan ‘Habu na Habu’ da Wanda ya Dace Mutane Su Zaba a 2023

Ya kara da cewa, wannan doka ta sabbin Naira ba sabuwa bace, tana nan a kasar nan tun shekaru biyar da suka shude.

Sanusi ya tona asirin sirrin da ke tattare da sauya kudin kasa
Sake Fasalin Naira Zai Fi Cutar Da ’Yan Siyasa Fiye da Talakawan Najeriya, Inji Sarki Khalifa Sanusi | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Da yake caccakar ‘yan siyasa, Sanusi ya ce ‘yan siyasar sun tara kudaden haram marasa amfani, suna son amfani da fushin ‘yan Najeriya wajen cimmam burinsu, rahoton Ripples Nigeria.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shawarwarin sarkin Kano Sanusi II game sabuwar dokar kudi

Ya ce:

“Dokar (dokar sauya fasalin kudi) na nan a kan hanya sama da shekaru 10. Kuma na Najeriya a shirye take da dokar tunda muna hanyoyin musayar kudi baya ga amfani da tsaba (kudin takarda ko na karfe).
“Shawari na biyu shine ‘yan Najeriya su kula da abin da ‘yan siyasa ke cewa. ‘Yan siyasa za su sha wahala daga wannan dokar fiye da talakawa.
“Sun shafe shekari hudu suna satar kudin kasa da kuma gallazawa mutane, duk da haka idan wani zaben yazo, sai su fitar da kudin su siya kuri’u da kayan tsaro ga jami’an INEC; kana su dauki nauyin ‘yan daba su dagule zaman lafiyan zabe.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Saura kiris zabe, Limaman Katolika sun fadi wadanda za su zaba a zaben bana

“Dokar za ta rage murdiya da sauran makamancinsa a lokacin zabe. Idan kana son ba jami’in INEC, dan sanda, alkali wasu kudi, ka tura ta bankuna inda za a iya ganewa da sauki.
“Ya kamata ‘yan Najeriya su marabci wannan sabuwar dokar saboda za ta basu damar zaben wanda suke so, ba wai wadanda za su yi hayar ‘yan daba ko su siya kuri’u a lokacin zabe ba.
“A baya, wadanda suka fi sata su ne ke yin murdiya su hau mulki. A yanzu ko da mutum na da buhin kudi, basu da amfani domin an sauya kudin.”

A wani labarin, Sanusi ya magantu kan shugabannin da ya kamata a zaba a zaben da ke tafe nan da kasa da mako guda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel