2023: Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Ya Yi Sabon Jawabi Ana Kwana 4 Zabe

2023: Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan Ya Yi Sabon Jawabi Ana Kwana 4 Zabe

  • Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi kira ga yan Najeriya su zama masu yarda da kaddara a yayin da ake tunkarar zabe
  • Jonathan ya kuma yi kira ga yan siyasa da su guji furta kalaman da za su tada rikici su kuma kyalle dimokradiyyar Najeriya ta girma
  • Tsohon shugaban kasar ya kuma yi kira ga matasa kada su yarda yan siyasa su yi amfani da su don cimma burinsu saboda mako ne da za su zabi wanda zai jagorance su

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi sabon jawabi gabanin zaben ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu na shugaban kasa da majalisar tarayya.

Tsohon shugaban kasar ya yi kira ga zaman lafiya a yayin da ya yi kira ga yan Najeriya masu kishin kasa su kasance cikin lumana tare da rungumar kaddara, Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu ko Obi: Kada Ku Zabi Yan Takara Saboda Coci Da Masallaci Sun Nemi Ku Yi Haka – Shehu Sani Ga Yan Najeriya

Goodluck
2023: Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Yi Sabon Jawabi Ana Kwana 4 Zabe. Hoto: Goodluck Ebele Jonathan
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jonathan ya yi magana kan zaben 2023

Jonathan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ofishinsa ta fitar a ranar Talata, 21 ga watan Fabrairu inda ya yi kira ga yan siyasa su yi watsi da kiyayya da rikici kuma su zama masu dattaku da zurfin tunani yayin yin harkokinsuu gabanin zaben don Najeriya ta tsira.

Dattijon kasar da aka sani da aikin wanzar da zaman lafiya a kasa da waje ya ce zaben na 2023 na da matukar muhimmanci ga yan Najeriya, yana mai cewa zabe lokacin gaskiya ne da kotu.

Abin da ke faruwa a baya-bayan nan kan tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, Kudu maso gabas, zaben 2023

Da ya ke kira ga matasa, Jonathan ya ce:

"Kasar ta ku ne a nan gaba; kada ku bari a yi amfani da ku wurin lalata kasa da tada rikici. Kune za ku gina Najeriya. Wannan zaben ya baku damar ku taka muhimmin rawa wurin zaben shugabannin da ku ke ra'ayi; wadanda za ku iya tambayar su idan basu cika alkawari ba, wadanda ku ka aminta za su kare muku kasarsu su tabbatar da hadin kai da zaman lafiya da cigaban kasar mu."

Kara karanta wannan

Allah Ya Sa Banki Su Karba: Matashi Ya Baje Kolin Tsabar Kudi Da Ya Dauki Shekaru Yana Ajiyewa a Gida

A cewarsa, kasancewar Najeriya kasa da ke demokradiyya hakan na nufin yan kasar ne za su zabi yadda makomarta za ta kasance, yana mai cewa demokradiyya ya bawa yan kasa iko a hannunsu.

Fitattun Fastoci 5 Da Ke Goyon Bayan Takarar Shugabancin Kasa Na Peter Obi

A bangare guda kun ji cewa wasu fitattun fastoci a Najeriya sun fito karara sun nuna goyon bayansu ga takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi.

Daga cikinsu akwai Fasto Chris Oyakhilome wanda ya ce an masa wahayi cewa Obi ne mafi alheri ga Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel