Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Nasarar Oyebanji a Zaben Gwamnan Ekiti

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Nasarar Oyebanji a Zaben Gwamnan Ekiti

  • Kotun daukaka kara a Edo Ekiti ta tabbatar da nasarar Oyebanji a zaben gwamnan Jihar Ekiti
  • Mista Oni, ɗan takarar gwamna a inuwar SDP ne ya kalubalanci sakamakon zaben wanda INEC ta sanar
  • A ranar 18 ga watan Yuni, 2022 aka gudanar da zaben gwamna a jihar, ɗan takarar APC ya samu naaara

Ekiti - Kotun daukaka kara mai zama a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, ta tabbatar da Biodun Oyebanji a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Idan baku manta ba hukumar zaɓe mai zaman kanta ta gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti ranar 18 ga watan Yuni, 2022, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Zaben Ekiti.
Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar da Nasarar Oyebanji a Zaben Gwamnan Ekiti Hoto: Biodun Oyebanji
Asali: Facebook

Da yake yanke hukunci ranar Talata, kwamitin Alƙalai uku na Kotun ya yi watsi da ƙarar wacce ɗan takarar gwamna a inuwar Social Democratic Party (SDP), Segun Oni, ya shigar yana kalubalantar sakamakon zaɓen.

Kara karanta wannan

"Wannan Cin Mutunci Ne" Gwamna Wike Ya Ƙara Fusata, Ya Yi Wa Atiku Tatas Ana Saura Kwana 5 Zabe

Kwamitin alkalan ya kori karar ɗan takarar jam'iyyar SDP ne saboda rashin cancanta da hurumin kalubalantar zaɓen.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sakamakon zaben Ekiti

INEC ta ayyana Oyebanji, tsohon sakataren gwamnatin jihar (SSG) a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun galaba a kananan hukumomi 15 daga cikin 16 da ke Ekiti.

Gwamna Oyebanji, wanda ya tsaya takara a inuwar jam'iyyar APC, ya samu kuri'u 187,057, hakan ya ba shi nasarar lallasa Mista Oni na SDP wanda ya samu kuri'u 82,211 da Bisi Kolawole na PDP wanda ya tashi da kuri'u 67,457.

Yadda shari'ar ta faro

The Cable ta ce bisa rashin gamsuwa da sakamakon zaben, Oni ya shigar da ƙarar Oyebanji da APC gaban Kotun sauraron kararrakin zaɓe karkashin mai shari'a Wilfred Kpochi.

A ƙarar, Mista Oni ya yi ikirarin cewa zaben da Oyebanji ya samu nasara cike yake da kura-kurai kuma kwamitin Mala Buni bai da ikon shirya zaben fidda gwani, wanda Oyebanji ya zama ɗan takarar APC.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Takarar Gwamna 3 Sun Janye, Sun Ayyana Goyon Bayansu Ga Sharada a Zaben 2023

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a ranar 29 ga watan Disamba, Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta kori karar. Daga nan ya tafi gaba zuwa Kotun ɗaukaka ƙara.

A wani labarin kuma Yan Takarar Gwamnan Kano Uku Sun Janye, Sun Koma Bayan Sha'aban Sharada

A daidai lokacin da zabe ke ƙara matsowa kusa, a jihar Kano tseren neman zama gwamna ya kara ɗumi fiye yadda ake tsammani.

Ɗan takara a jam'iyyar ADC, Sha'aban Sharada, ya kara karfi bayan ya karbi 'yan takarar gwamna uku da jam'iyyu daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel