APC Na Da Jihohi 21, PDP Jan Ragamar Jihohi 14 Gabannin Zaben 2023
Ana gab da babban zaben Najeriya na 2023 inda za a fara da zaben shugaban kasa da na yan majalisar dokokin tarayya a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.
Yanzu haka, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ce mai mulki a kasar yayin da Peoples Democratic Party (PDP) ke matsayin babbar jam'iyyar adawar kasar.

Asali: Twitter
Gabannin zaben, jam'iyyar APC mai mulki na jan ragamar jihohi 21 yayin da PDP mai adawa ke shugabanci a jihohi 14, ciki harda na baya-bayan nan, Osun (wacce ake jiran kotu ta yanke hukuncin karshe).
Jiha daya da ta yi saura, Anambra, jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ce ke shugabanci a cikinta.
Yanzu abun da ya saura shine jiran tsammani don ganin ko yanayin siyasar zai chanja bayan zabe musamman kasancewar PDP ta dauki matakai na ganin ta kwato shugabancin kasar.

Kara karanta wannan
Zaben Gwamnan Ogun: Jam’iyyun Siyasa 10 Da Mambobin APC Sun Yi Maja Da PDP Don Tsige Gwamnan APC Daga Mulki
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka kuma, jam'iyyar Labour Party ma tana nan tana ta shirya dabarun tunkudar da manyan jam'iyyun kasar biyu.
Babban zaben 2023: Jihohin da APC da PDP ke jagoranta
- Abia - PDP
- Adamawa - PDP
- Akwa Ibom - PDP
- Anambra - APGA
- Bauchi - PDP
- Bayelsa - PDP
- Benue - PDP
- Borno - APC
- Cross River - APC
- Delta - PDP
- Ebonyi - APC
- Edo - PDP
- Ekiti - APC
- Enugu - PDP
- Gombe - APC
- Imo - APC
- Jigawa - APC
- Kaduna - APC
- Kano - APC
- Katsina - APC
- Kebbi - APC
- Kogi - APC
- Kwara - APC
- Lagos - APC
- Nasarawa - APC
- Niger - APC
- Ogun - APC
- Ondo - APC
- Osun - PDP
- Oyo - PDP
- Plateau - APC
- Rivers - PDP
- Sokoto - PDP
- Taraba - PDP
- Yobe - APC
- Zamfara - APC

Kara karanta wannan
Zaben 2023: Kotu Ta Bada Sabuwar Hukunci A Karar Da PDP Ta Shigar Kan Tinubu Da Shettima
Kada ku yi zaben tumun dare - Shehu Sani ya gargadi yan Najeriya gabannin zaben 2023
A wani labarin, tsohon sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yi gagarumin jan hankali ga yan Najeriya yan kwanaki kafin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Sani ya shawarci yan kasar da su yi aiki da hankali wajen zabar shugabanninsu sannban kada su zabi dan takara saboda coci ko masallacin da suke bi ya bukaci su yi haka.
Tsohon dan majalisar ya ce duk wani zaben tumun dare da za a yi a ranar Asabar daidai yake da lalube cikin duhu na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
Asali: Legit.ng