Jerin Sunayen Ƴan Takarar Da Suka Mutu Ana Gab Da Zaɓen 2023

Jerin Sunayen Ƴan Takarar Da Suka Mutu Ana Gab Da Zaɓen 2023

  • Ƴan takara da dama a.ƙarƙashin jam'iyyun daban-daban a ƙasar nan sun rigamu gidan gakiya
  • Rasuwar su ta sanya dole jam'iyyun da suke takara a ƙarƙashin su, sake gudanar da zaɓen fitar da gwani
  • Wasu daga cikin ƴaa takarar sun mutu ne a dalilin rashin lafiya, hatsarin mota, yayin da wasu kuma halaka su aka yi

A yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023, wasu ƴan takarar da suka yi niyyar yin takarar tun daga kan kujerar gwamna, har zuwa ta ƴan majalisu sun rigamu gidan gaskiya.

Mutuwar ta su dai na nufin jam'iyyun su sai sun sake yin zaɓen fitar da gwani domin samar da waɗanda za su maye gurbin su, musamman a kujerun gwamnoni. Rahoton Legit.ng

Hanarabul Ado
Dan Ƴan Takarar Da Suka Mutu Ranar Litnin Hoto: Rabiu Kwankwaso/NNPP
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ana Saura Kwana 3 Zaɓe, Atiku Ya Sha Wani Babban Alwashi Kan Tinubu

Ga jerin wasu daga cikin ƴan takarar da suka rigamu gidan gaskiya kafin zaɓe:

  1. Uchenna Ikonne, ɗan takarar gwamnan jihar Abia na jam'iyyar PDP

Ɗan takarar gwamnan jihar Abia a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP, Uchenna Ikonne, ya mutu ne a ranar Laraba, 25 ga watan Janairun 2023.

2. Alhaji Aliyu Maina, ɗan takarar gwamnan jihar Adamawa na jam'iyyar NRM

Haka kuma, ɗan takarar gwamnan jihar Adamawa a jam'iyyar NRM, ya rasu a ranar Laraba, 25 ga watan Janairun 2023.

An tabbatar da rasuwar Maina ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Janairu. Ya rasu ne a gidan sa dake birnin tarayya Abuja, bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya.

3. Chukwunonye Irouno, ɗan takarar ɗan majalisar jiha na jam'iyyar Labour Party, a jihar Imo

Chukwunonye Irouno, ɗan takarar kujerar majalisar jiha na ƙaramar hukumar Okigwe a jihar Imo, ya mutu ne a ranar Litinin, 5 ga watan Disamban 2022.

Kara karanta wannan

Saura Kwana 3 Zabe, Kamfen Tinubu Ya Samu Tagomashin Manyan Fastoci 100

Iruno wanda hadimi ne ga tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha, ya mutu jim kaɗan bayan ya iso gidansa dake a birnin Owerri.

4. Christopher Elehu, ɗan takarar ɗan majalisar jiha na jam'iyyar Labour Party, a jihar Imo

Haka kuma Christopher Elehu, ɗan takarar kujerar majalisar jiha na ƙaramar hukumar Onuimo a jihar Imo, ya mutu bayan wasu mahara sun halaka shi a ranar Juma'a, 16 ga watan Disamban 2022.

5. Barrista Abba Bello Haliru, ɗan takarar majalisar wakilai na jam'iyyar PDP a jihar Kebbi

Barrista Abba Bello Haliru, ɗan takarar jam'iyyar PDP a mazaɓun Birnin Kebbi/Kalgo/Bunza a majalisar wakilai, ya rasu a ranar Juma'a, 6 ga watan Janairun 2023, a birnin tarayya Abuja. Ya rasu ne bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya.

6. Mathew Akawu, ɗan takarar ɗan majalisar jiha na jam'iyyar PDP a jihar Filato

Mathew Akawu, ɗan takarar jam'iyyar PDP a majalisar jihar Filato, ya mutu a safiyar ranar Juma'a, 6 ga watan Janairun 2023, bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Hamshaƙan Attajirai 6 Dake Takara a Zaɓen 2023

7. Ejikeme Omeje, ɗan takarar majilisar wakilai na jam'iyyar APC a jihar Enugu

Pharm. Ejikeme Omeje, ɗan takarar jam'iyyar APC a mazaɓun Nsukka/Igbo-Eze ta Kudu, a majilisar wakilai, ya mutu a watan Nuwamban 2022.

Omeje, ya mutu ne a wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a ranar Talata, 8 ga watan Nuwamba.

8. Kamilu Ado Wudil

Kamilu Ado Wudil wanda yake neman zama ‘dan majalisar tarayya a zabe mai zuwan nan.

Darektan kafofin sadarwa na zamani na kwamitin yakin zaben NNPP a jihar Kano, Salisu Yahaya Hotoro ya yi maganar wannan rasuwa a jiya.

Yin Koyi Da Yesu: Fasto Ya Mutu Yana Tsaka Da Azumin Kwana 40

A wani labarin na daban kuma, wani fasto mai ƙoƙarin yin koyi da azumin Yesu Almasihu, ya sheƙa barzahu.

Faston dai yayi ƙoƙarin yin azumin kwana 40 kamar yadda aka bayyana Yesu yayi a cikin littafi mai tsarki na addinin kirista.

Asali: Legit.ng

Online view pixel