Siyasar Najeriya
Majalisar wakilai ta rantsar da sababbin mambobi uku daga zaben cike gurbi na Agusta 2025, APC ta samu kujeru hudu, PDP daya, yayin da ya rage saura kujeru biyu.
Rahotanni sun nuna cewa shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark na jagorantar wani taro da sauran jagororin jam'iyyar domin ci gaba da shirye shiryen 2027.
Mawaki Dauda Abdullahi Kahutu Rarara da amaryarsa sun gana da Bola Ahmed Tinubu inda suka nuna goyon baya ga shugabancinsa mai adalci a Najeriya.
Jam'iyyun siyasa da aka yi wa rajista sun nuna damuwarsu kan batun zaben sabon shugaban hukumar INEC. Sun bayyana cewa bai kamata shugaban kasa ya zabe shi ba
Paul Ibe, hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci Tinubu ya tsige Uche Nnaji daga matsayin Ministan Kimiyya da Fasaha.
Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta yi tsokaci kan zargin da ake yi wa minista a gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, kan yin amfani da takardun bogi.
Tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomhole, ya ja kunnen tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan kan yin takarar a babban zaben shekarar 2027.
Jigon jam'iyyar APC, Salihu ISa Nataro da ya yi takarar gwamna a jihar Kebbi ya bukaci Aliko Dangote da gwamna Alex Otti su fito takara a zaben 2027 mai zuwa.
Ministan makamashi, Bayo Adelabu ya ce lokaci ya yi da zai mulki Oyo, yayin da bayyana niyyarsa ta yin takarar gwamna a 2027 bayan shan kaye a 2019 da 2023.
Siyasar Najeriya
Samu kari