Wike Ya Sake Ɓantaro wa PDP Aiki, Ya Fadi Yadda Tinubu Zai Lashe Zabe a 2027

Wike Ya Sake Ɓantaro wa PDP Aiki, Ya Fadi Yadda Tinubu Zai Lashe Zabe a 2027

  • Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, ya ce PDP ba za ta iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a 2027 ba idan ba ta canza tsari ba
  • Ya zargi PDP da karya kundin tsarin mulkinta a 2023 ta hanyar ba da tikitin shugaban ƙasa da na shugaban jam'iyya ga shiyyar Arewa
  • A cewar Nyesom Wike, idan har jam'iyyar PDP ta sake maimaita kuskuren da ta yi 2023 to za ta sake shan kasa a zaben 2027 mai zuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce jam’iyyarsa ta PDP, ba za ta samu nasara kan Shugaba Bola Tinubu a 2027 ba, idan ba ta canza tsarin ba da tikiti ba.

Ministan ya yi wannan bayanin ne a yayin wata tattaunawa ta kai tsaye da kafafen yaɗa labarai a ranar Litinin, a babban birnin tarayya, Abuja.

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce PDP za ta sha kasa a 2027 idan ba ta canja tsarin rabon mukamai ba
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike. Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Wike ya zargi PDP da take dokokin jam'iyyar

Wike ya ce yanzu an daina bin tanadin kundin tsarin mulkin PDP, wajen raba kujerar shugaban jam'iyya da tikitin takarar shugaban ƙasa ga shiyyoyi, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da shugaban kwamitin amintattu na PDP, Adolphus Wabara, ya karɓi tsofaffin gwamnoni Samuel Ortom (Benue), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), da wasu mutane 38 zuwa cikin kwamitin.

A lokacin rantsar da su, Adolphus Wabara ya yi kira ga sababbin mambobin da su taimaka wajen jagorantar PDP zuwa tudun-mun-tsira, inda ya cehar yanzu jam’iyyar na da karfinta.

Sai dai, Wike ya zargi wasu mambobin kwamitin amintattu da cewa sun yi amfani da tanadin kundin mulkin jam’iyyar don son kai a lokacin babban zaɓen 2023.

A cewarsa, jam'iyyar ta ba Atiku Abubakar tikitin takarar shugaban ƙasa, ta kuma zabi Iyorchia Ayu matsayin shugaban jam'iyya, waɗanda dukansu suka fito daga yankin Arewa.

Wike ya gargadi PDP kan maimaita kuskuren 2023

Vanguard ta rahoto ministan babban birnin tarayyar, ya gargadi PDP kan cewa idan har ta sake maimaita irin wannan kuskuren a 2027, to za ta sha kasa hannun APC.

Nyesom Wike ya gargadi PDP da ka da ta maimaita kuskuren da ta yi a zaben 2023
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike. Hoto: @GovWike
Asali: Facebook

Mun ruwaito Nyesom Wike ya na cewa:

“Zan sake maimaita wa, idan har PDP ba ta yi taka-tsan-tsan ba, to ku jira ku ga abin da zai faru. Kuna sane da cewa son kai zai iya kashe jam'iyyar.
"Mu faɗa wa kanmu gaskiya; a 2023, mun faɗa wa jam’iyyar, cewa a kundin tsarin mulkinmu, an amince cewa idan wannan shiyya ta dauki shugaban jam'iyya to waccan shiyyar za a ba takarar shugaban kasa.
“Amma saboda son zuciya, suka ce a’a, kada a ce za a kawo batun rabon shiyya yanzu. Kafin mu ankare, wasu mutane sun je sun sayi fom. Amma me ya faru daga karshe? Kowa ya gani."

Wike ya fadi raunin Siminalayi Fubara

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce ya gana da Siminalayi Fubara tare da wasu gwamnoni biyu na APC.

Wike ya bayyana rashin gamsuwar cewa Fubara na da ikon kawo zaman lafiya, inda ya soki yadda magoya bayansa ke ci gaba da tayar da hankali a jihar Ribas.

A nasa ɓangaren, Fubara ya bukaci magoya bayansa da su daina ɗaukar matakai a madadin sa, yana mai cewa wasu ayyukan na su na barazana ga sasanta rikicin da ya fara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.