"Ba Ni da Tabbacin Ci Gaba da Zama a PDP," Gwamna Ya Nuna Alamun Sauya Sheƙa kafin 2027
- Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya sake nuna alamun zai fice daga jam'iyyar PDP gabanin babban zaɓen 2027
- Gwamna Eno ya ce a halin yanzun bai san wace jam'iyya zai koma ba a nan gaba, amma ya tabbatarwa al'ummar jihar cewa zai yi wa kowa adalci
- Umo Eno ya nanata cewa shi gwamna ne na kowane dan Akwa Ibom ba tare da la'akari da jam'iyyun siyasa ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Almu sun nuna cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, na dab da kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa zai sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Gwamna Umo Eno ya bayyana cewa a halin da ake ciki yanzu, bai san wace jam'iyyar siyasa zai koma ba nan gaba amma ya yi alƙawarin zama gwamnan kowa a Akwa Ibom.

Asali: Twitter
A rahoton da Premium Times ta buga, Fasto Eno ya ce siyasa na iya canza wa a kowane lokaci idan aka duba masalahar al'ummar da ake jagoranta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ya tabbatar wa al'umma cewa zai ci gaba da jagorantarsu ba tare da nuna banbanci tsakanin ƴaƴan APC, PDP ko YPP ba.
Gwamna Eno ya bayyana hakan ne a wani taron yabo da godiya da aka shirya masa a cocin The Apostolic Church, da ke jihar Legas, ranar Lahadi.
Wace jam'iyya Gwamna Eno zai koma?
Da yake jawabi a cocin, Gwamna Eno ya ce:
"Ban san inda zan kasance gobe ba, ko a PDP, APC, ko YPP. Wadannan dai suna daga cikin dandalin siyasa ne kawai amma ba su ne za su tantance wanene ni ba.
"Zan ci gaba da aiki a matsayin gwamna na kowa ba tare da la'akari da banbancin jam'iyyun siyasa ba, zan ci gaba da haɗa kan jam'iyyu ko da kuwa na sauya sheƙa."

Asali: Facebook
Gwamna Eno zai ci gaba da zama a PDP?
Sai dai Umo Eno jaddada cewa ba yana nufin kai tsaye zai fice daga PDP ba ne, amma yana kokarin fahimtar da jama'a yanayin siyasa na iya sauyawa a ko da yaushe.
Gwamnan ya yi nuni da cewa ya kamata ‘yan siyasa su zama kamar ’ya ’yan Issachar da aka faɗa a Littafi Mai Tsarki, wadanda suke duba zamani da yanayi don su yanke shawarar da ta dace.
Duk da cewa bai bayyana a fili cewa zai sauya sheƙa ba, Gwamna Umo Eno ya nuna karara cewa ƙofarsa a buɗe take, yana kuma buƙatar goyon baya daga kowace jam’iyya, muddin hakan zai kawo ci gaba ga jihar Akwa Ibom.
"PDP da APC duk manufarsu 1" - Umo Eno
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Umo Eno ya bayyana cewa jam'iyyun siyasa ba su da banbanci domin duk manufarsu guda ɗaya ce ta neman nasara a zaɓe.
Gwamna Eno ya yi ikirarin cewa da APC da PDP duk abu guda ne domin manufarsu ɗaya a siyasar Najeriya.
Ya kuma kalubalanci duk wani ɗan Najeriya da ke ganin baa haka bane da ya nuna masa banbancin manufofin jam’iyyun siyasar kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng