Ana Shirin Nakasa PDP, Gwamnoninta Sun Yi Barazanar Ficewa daga Jam'iyya

Ana Shirin Nakasa PDP, Gwamnoninta Sun Yi Barazanar Ficewa daga Jam'iyya

  • Bangaren Kudu maso Gabas na PDP ya yi barazanar ficewa daga jam’iyya idan ba a nada Sunday Udeh-Okoye a matsayin Sakatare ba
  • Barazanar na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun manyan jam'iyyun adawa, musamman PDP na ficewa zuwa jam'iyya mai mulki
  • Jagorori a Kudu maso Gabas suna zargin uwar jam'iyyarsu ta kasa da rashin daukar bukatun da suka gabatar mata da daraja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Sabuwar barazana daga yankin Kudu maso Gabas, wacce za ta iya yiwa PDP babban lahani ta kunno kai cikin jam'iyyar.

Wannan na zuwa ne kasa da kwanaki uku bayan shugabannin jam’iyyar sun cimma matsaya na yin tafiya tare da nada kwamitin Bukola Saraki da zai ceto PDP.

Jamiyya
Gwamnonin PDP na Kudu maso Gabas na sun gargadi jam'iyyarsu Hoto: Bala Mohammed
Asali: Twitter

The Nation ta wallafa cewa gwamnoni a yankin Kudu maso Gabas a sun yi barazanar ficewa daga jam’iyyar idan har ba a nada tsohon Shugaban Matasa na Kasa, Sunday Udeh-Okoye, a matsayin Sakataren Jam’iyya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar jagororin PDP na yankin ta tunatar da cewa tun bara suka amince da Udeh-Okoye ya rike mukamin, amma aka yi watsi da bukatarsu.

Gwamnonin PDP sun yiwa jam’iyyar barazana

Channels TV ta ruwaito cewa bangaren Kudu mas o Gabas na PDP ya ce an tsayar da Udeh-Okoye ne domin ya kammala wa’adin tsohon Sakataren kamar yadda aka tsara.

Jagororin sun yi gargaɗi ga jam’iyyar cewa kada ta ɗauki yankin da wasa, domin hakan na iya jawo wa jam’iyyar gagarumar matsala.

Damagum
Wasu gwamnonin PDP sun ce za su bar jam'iyya Hoto: Umar Iliya Damagum
Asali: Twitter

Cikin wadanda suka halarci wannan taron har da Gwamnan Enugu, Peter Mbah da Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP, Sanata Adolphus Wabara.

Sauran sun hada da tsohon Gwamnan Imo, Achike Udenwa da Mataimakin Shugaban PDP na Kudu maso Gabas, Cif Ali Odefa.

Sun bayyana fushinsu da yadda shugabancin PDP ke tafiyar da al’amuran jam’iyyar a taron shugabannin zartarwa na PDP na Kudu maso Gabas da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar Enugu.

Jagororin PDP sun nemi a hada kai

Mbah, wanda ke jagorantar jam’iyyar a shiyyar, ya bukaci ci gaba da hadin kan yankin, tare da jaddada bukatar yin magana da murya daya domin cimma burinsu na siyasa.

A nasu bangaren, Sanata Wabara da tsohon gwamna Udenwa sun koka kan abin da suka kira rashin girmama Kudu maso Gabas da PDP ke yi.

Sai dai ma’aikatan hedkwatar PDP ta kasa da ke Abuja sun sake jaddada goyon bayansu ga nada Setonji Koshoedo, a matsayin mukaddashin Sakataren Jam’iyya.

Rigimar shugabancin PDP ta fara ne shekaru biyu da suka gabata, lokacin da tsohon sakatare, Sanata Samuel Anyanwu, ya dawo domin karɓar matsayin nasa da ya bari.

Gwamnonin PDP za su sauya sheka

A wani labarin, kun ji cewa ana zargin gwamnoni hudu na PDP na shirin sauya sheka zuwa APC domin marawa Shugaba Bola Tinubu baya a yunkurinsa na sake tsayawa takara a 2027.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa gwamnonin sun soma shirye-shiryen barin jam’iyyarsu ta PDP domin shiga cikin tafiyar hadin kan siyasa da ke ƙara karfi gabanin babban zabe na gaba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar rudani daga wasu jihohin Arewacin Najeriya, inda ake samun barazanar janye goyon baya ga Shugaba Tinubu a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.