Hukumar EFCC Ta Cafke Malaman Addinin Musulunci da Limaman Coci a Najeriya

Hukumar EFCC Ta Cafke Malaman Addinin Musulunci da Limaman Coci a Najeriya

  • Shugaban hukumar EFCC na kasa, Ola Olukoyede ya ce sun kama malaman addinin musulunci da limaman coci kan zargin zamba
  • Olukoyede ya ce wasu daga cikinsu na tsare a wurin ajiyar wadanda ake zargi na EFCC yayin da wasu kuma kotuna sun yanke masu hukunci
  • Ya ce aikata laifuffakan cin hanci da rashawa bai takaita kan 'yan siyasa kadai ba, akan samu irin hakan a kungiyoyin addini a Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) ta bayyana cewa tana tsare da malaman adidnin musulunci da na kiristoci kan laifuffukan da suka shafi zamba.

Shugaban hukumar EFCC na kasa, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa a halin yanzu akwai shugabannin addini da dama ciki har da Fastoci da Limamai a hannunsu.

Kara karanta wannan

EFCC ta gano yadda kudin kasashen waje ke sauka kamar ruwan sama a asusun malami a Najeriya

Shugaban EFCC.
Shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Ola Olukoyede a ofishinsa da ke Abuja Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

EFCC na tsare da malamai da fastoci

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa shugaban na EFCC ya fadi hakan ne a wurin taron bayar da tallafin kasuwanci na gidauniyar Fasto Jerry Eze da aka yi a Abuja ranar Laraba.

Ya kuma bayyana cewa tuni aka yanke wa wasu daga cikin malaman da EFCC ta cafke hukunci bayan gurfanar da su a gaban kotu.

A cewarsa, cin hanci da rashawa bai takaita kan siyasa ko kamfanoni kadai ba. Ya jaddada cewa hkungiyoyin addini ma sun shiga cikin jerin wadanda ake gudanar da binciken yaki da rashawa a kansu.

Yadda EFCC ke hukunta malaman addini

"A yanzu da nake wannan maganar muna da (malamai da fastoci) da yawa a wurin ajiyar wadanda ake zargi. Wasu daga cikinwadanda muka kama an riga da an yanke masu hukunci kan zamba," in ji shi.

Olukoyede ya bayyana cewa ya kamata a kalli munanan ayyuka da wasu ke aikatawa a matsayin gazawar mutum a karan kansa, ba wai a matsayin abin da ke nuna gaskiyar addininsa ba.

Kara karanta wannan

Mutanen jihar Kano na cikin alheri a mulkin Tinubu, an raba wa talakawa Naira biliyan 48

EFCC tana tabo kungiyoyin addinai

Shugaban na EFCC ya kara da cewa:

"Kungiyoyin addini a kasar nan, kamar na Kirista da na Musulunci na iya fuskantar barazanar cin zarafi ko tafka ba daidai ba. Ayyukan mu na yaki da rashawa suna shiga har kan mimbari da kuma cikin masallaci."

Wannan bayani na Olukoyede ya tabo tanadin dokar harkokin kamfanoni da sauran al'amuran da suka shafi hakan (CAMA), kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.

Dokar, wacce aka sanya wa hannu a shekarar 2020, ta bai wa hukumomi kamar EFCC damar shiga cikin lamuran kungiyoyin addini idan ana zargin zamba, rashin gudanarwa nagari, ko rashin adalci.

Jami'an EFCC.
Jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) a bakin aiki a Najeriya Hoto: EFCC Nigeria
Source: Getty Images

EFCC ta yi bincike kan Fasto Jerry Eze

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC ta gano yadda ake turo Dalolin Amurka da kudin Ingila zuwa asusun Fasto Jerry Eze daga kasashe daban-daban.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa ya shafe watanni shida yana binciken Fasto Jerry Eze kan zargin halasta kudin haram.

Bayan kammala bincike, Olukoyede ya ce faston ya bayyana masa yadda kudaden ke shigowa da kuma yadda yake amfani da su wajen taimakon jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262