An Rarrashi Yar Tsohon Shugaban Kasa da Aka Buge Ta a Neman Takarar Gwamna
- Sanata Solomon Adeola ya sayi fom din takarar gwamnan jihar Ogun domin tsayawa takara a zaben shekarar 2027
- Adeola ya kai ziyara wajen Iyabo Obasanjo domin neman goyon bayanta bayan jam’iyyar APC ta ayyana shi a matsayin ɗan takara
- Iyabo Obasanjo ta dakatar da burinta na takarar gwamna bayan tsarin sulhu na APC, duk da cewa ta nuna damuwa da hakan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abeokuta, Ogun - Sanata Solomon Adeola mai wakiltar Ogun ta Yamma ya gana da Iyabo Obasanjo domin neman goyon bayanta.
Sanata Adeola ya kai ziyarar ce gabanin zaɓen gwamnan Ogun na shekarar 2027 duba da cewa ita ma ta nuna sha'awar neman takarar gwamna.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da faifan bidiyo da sanatan ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Laraba 29 ga watan Afrilun 2026.
Sanata Solomon Adeola ya ziyarci Iyabo Obasanjo
Yayin ziyarar, Adeola ya yaba wa Iyabo bisa abin da ya kira dattako da karɓar shawarar jam’iyya cikin fahimta.
A ranar 13 ga Afrilun 2026, gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, ya ayyana Adeola a matsayin ɗan takara na jam’iyyar APC domin neman gwamna.
Da yake magana a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Abeokuta, gwamnan ya ce an ɗauki matakin ne bayan doguwar tattaunawa domin tabbatar da haɗin kai da ci gaba a APC.

Source: Facebook
Iyabo ta nuna sha'awar takarar gwamna
Iyabo Obasanjo, diyar tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, ta nuna sha’awar tsayawa takarar gwamna kafin daga bisani ta dakatar da burinta.
Sai dai ta nuna damuwa kan yadda aka gudanar da tsarin, inda ta yi zargin cewa an hana wasu daga cikin magoya bayanta shiga wajen taron.
A ranar Talata 28 ga watan Afrilun 2026, Adeola ya kai mata ziyara tare da tsofaffin mataimakan gwamnoni Segun Adesegun da Salmot Badru da sauran jiga-jigan jam’iyyar.
Ya ce:
“Bayan jam’iyya ta zaɓe ni a matsayin ɗan takarar sulhu, ‘yar uwata Iyabo Obasanjo ta fitar da sanarwa tana goyon bayan jam’iyya tare da alƙawarin yin aiki tare da ni.
“Ba zan ba ki kunya ba. Mutanenki za su kasance cikin tarukanmu, kuma babu wanda za a bari a baya.”
Adeola ya ƙara da cewa zai tabbatar da haɗa magoya bayan Iyabo cikin harkokin jam’iyya da yanke shawara domin kada a ware kowa.
A martaninta, Iyabo Obasanjo ta ce ta riga ta umurci magoya bayanta su yi aiki domin nasarar APC a Ogun.
Ta kuma yi alƙawarin goyon bayan Solomon Adeola, sake zaɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC.
Iyabo Obasanjo ya gana da Bola Tinubu
A baya, an ji cewa yar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ta gana da Shugaba Bola Tinubu a Lagos inda ta yaba da jagorancinsa.
Iyabo Obasanjo ta jaddada kudirinta na tsayawa takarar gwamnan Ogun a zaben 2027 mai zuwa a jam'iyyar APC.
Ta bayyana cewa tattaunawarsu ta mayar da hankali kan shugabanci, inganta dimokuradiyya da ci gaban kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


