Dabaru 4 da Tinubu, Ganduje Suka Dauka wajen Ragargaza 'Yan Adawa

Dabaru 4 da Tinubu, Ganduje Suka Dauka wajen Ragargaza 'Yan Adawa

Masana da masu sharhi kan al’amuran siyasa irinsu Malam Kabiru Sufi na Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a a Kano, da Dakta Mukhtar Bello Maisudan na BUK, na ganin cewa an samu sauyin sheka mafi girma a tarihin Najeriya.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – A cikin ‘yan kwanakin nan, an samu sauyin sheka masu daukar hankali, bayan da zababben gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, tsohon gwamna Ifeanyi Arthur Okowa, da magoya bayansu suka koma APC.

Haka kuma, jam'iyyar mai mulki ta sake karɓar sababbin masu sauya sheƙa daga jam'iyyar hamayya ta PDP a jihar Kebbi, inda duka ‘yan majalisar dattawan jihar suka koma APC.

Tinubu
Yadda Tinubu da Ganduje ke ragewa yan adawa karfi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

BBC Hausa ruwaito cewa masana harkar siyasa sun ce ba a samun irin wadannan muhimman sauye-sauye haka kawai; akwai wasu dabaru hudu na Bola Tinubu da shugaban APC, Abdullahi Ganduje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun haɗa da:

1. Tinubu, APC na tsorartar da 'yan siyasa

A cewar Dakta Mukhtar Bello Maisudan, malamin jami’a kuma masani a harkokin siyasa, jam’iyya mai mulki kan yi amfani da wasu hukumomi wajen tsoratar da ‘yan adawa.

Ya kara da cewa wannan tsoratarwa na amfani a kan wasu daga cikin jagororin siyasa masu 'tabo' na zargin almundahana a baya.

Ya bayyana cewa:

"Ana ganin kamar ita jam'iyya da shugaba Tinubu da magoya bayansa na amfani da wasu hukumomi ta hanyar amfani da tsaoratar da manyan ƴaƴan jam'iyyun hamayya da suka taɓa riƙe muƙamai a baya kuma suka yi wa-ka-ci wa-ka-tashi kuma ana riƙe da fayil-fayil ɗinsu.
“Wannan zai iya jayowa a hura musu wuta cewa idan ba su goya wa shugaban ƙasa baya ba to za a yi musu bita da ƙulli - ba lallai mutum ya sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki ba. Zai iya zama a inda yake amma zai bayar da goyon baya.”

2. 'Tinubu na kunnawa 'yan adawa rikici,' Masani

Dakta Maisudan ya nuna cewa rikicin da ke faruwa a jam’iyyun hamayya na da alaƙa da sauyin sheƙar da ake gani a yanzu.

Masani a fannin siyasar kasar nan ya kara da cewa jam’iyya mai mulki ta APC na da hannu a tayar da wadannan rikice-rikice.

Ganduje
Ana zargin APC na kunna rikici a jam'iyyun adawa Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

A kalamansa:

"Idan ka kalli PDP ta zama mushen gizaka. Haka ma jam'iyyar LP ita ma an kunno mata rikici tsakanin ɓangarori biyu. Ita ma jam'iyyar NNPP ta rabu gida biyu.
Ba sabon abu ba ne. Idan jam'iyya na mulki to za ka ga za ta iya yin komai wajen goyawa wasu baya a cikin jam'iyyun hamayya domin rura musu rikici."

3. Alakar Tinubu, Ganduje da manyan yan siyasa

Malam Kabiru Sufi, masanin siyasa daga Kwalejin shirin shiga jami'a da ke Kano, ya ce shugaban kasa da APC na amfani da manyan yan siyasa wajen jawo wasu zuwa jam'iyyarsu.

A cewarsa, shugaba Tinubu na iya haɗa kai da manyan ‘yan siyasar yankuna, kamar gwamnoni don jawo manyan abokan hamayya zuwa APC, kamar yadda aka gani a jihar Kebbi.

4. Tinubu na yin romon baka ga 'yan siyasa

Sufi ya yi zargin cewa ana yin wasu alƙawura masu ɗaukar hankali ga ‘yan siyasa daga ɓangarorin hamayya domin jawo su zuwa APC, musamman ta hanyar ba su dama don amfanar da al’ummarsu.

Ya ce lokuta da dama waɗanda suka sauya sheƙa sun tabbatar da hakan, inda suka ce sun sauya jam’iyya ne don su sami damar cika wa jama’arsu alkawura.

Har ila yau, ana zargin gwamnatin Tinubu da yi wa wasu ‘yan siyasa alkawarin tsayawa takara, samun mukamai da kuma damar shiga cikin harkokin gwamnati.

Idan za a iya tunawa, Sanata AbdulRahmad Kawu Sumaila daga Kano ya bayyana cewa dalilinsa na barin NNPP zuwa APC shi ne domin:

“Zai kara samawa mutane na ayyuka da ba zan iya samu a nan (NNPP) ba.”

Gwamnan Delta da mutanensu sun koma APC

A baya, kun samu labarin cewa a wani lamari mai ɗaukar hankali a siyasar Najeriya, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Ya sanar da haka a ranar Laraba, 15 ga Mayu, bayan wata ganawa ta sirri da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Asaba, jihar Delta, inda manyan shugabannin APC suka karɓe shi.

Gwamnan ya ce sauya shekar da ya yi zai kara tabbatar da haɗin gwiwa da ci gaban jihar Delta a matakin ƙasa, kuma wannan ba zai kawo matsala a gudanar da gwamnatinsa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.