"Ka Watsar da PDP idan Kana Son Ci Gaban Al'ummarka," An Buƙaci Gwamna Ya Koma APC

"Ka Watsar da PDP idan Kana Son Ci Gaban Al'ummarka," An Buƙaci Gwamna Ya Koma APC

  • Udengs Eradiri ya bukaci Gwamna Douye Diri da Sanata Dickson sun haƙura da PDP, su jagoranci ƴan ƙabilar Ijaw zuwa APC
  • Tsohon ɗan takarar gwamnan ya ce lokaci ya yi da kabilar Ijaw za ta shiga a dama da ita a harkokin gwamnatin tarayya
  • Ya ce hakan za ta tabbata ne idan sun koma jam'iyyar APC mai mulki, idan kuma ba haka ba, za a ware su a gefe guda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa - Tsohon ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar LP a jihar Bayelsa, Udengs Eradiri, ya bukaci Gwamna Douye Diri da wanda ya gada, Sanata Seriake Dickson su haɗe da gwamnatin tarayya.

A wata sanarwa da ya fitar a Yenagoa a ranar Laraba, Eradiri ya ce wannan shi ne lokacin da ya dace ƴan kabilar Ijaw su rungumi jam'iyyar APC.

Gwamna Douye Diri.
Eradiri ya bukaci gwamnan Bayelsa da shugabannin PDP su koma APC Hoto: Douye Diri
Asali: Twitter

Eradiri ya bayyana wannan lokaci a matsayin “lokacin da ake sauya fasalin siyasa a Najeriya," kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ƴan ƙabilar Ijaw na iya fuskantar koma baya idan har Gwamna Diri da Sanata Dickson suka gaza fahimtar gaskiya, su jagorance su zuwa APC.

An bukaci Gwamna Diri ya koma APC

Injiniya Eradiri ya bukace su da su sauya sheka daga PDP zuwa APC domin samun damar da ƙabilar Ijaw za ta taka rawa a harkokin mulki a matakin ƙasa.

Eradiri, tsohon shugaban ƙungiyar matasan Ijaw ya ce shiga jam’iyyar APC zai sake buɗe wa jama'a ƙofar samun ƙarin ababen more rayuwa da inganta walwalarsu.

“Babu wani alheri da ƙabilar Ijaw za ta samu idan ta zauna a tsagin adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Abin da hakan zai haifar kawai shi ne a ware mu daga siyasar ƙasa,” in ji shi.

Eradiri ya bukaci shugabnnin Bayelsa su cire son rai

Bisa haka ne, tsohon ɗan takarar ya roƙi Gwamna Diri da Dickson su cire son rai su dubi maslahar ƙasa da al’ummarsu, su watsar da PDP kana su koma APC.

“Lokacin sake tsara siyasar ƙabilar Ijaw ya yi. Idan ba mu yi shiri da wuri muka shiga APC ba, to za a ware mu gefe a siyasar Najeriya.
“Don haka, na ke kira ga Sanata Dickson da Gwamna Diri su koma APC domin bai wa ƙabilar Ijaw damar shiga cikin harkokin mulki a matakin ƙasa.”

Eradiri ya kara da cewa babu fa’ida a cigaba da adawa da gwamnatin Tinubu, domin hakan zai hana ƙabilar Ijaw samun wakilci a gwamnati, rahoton Vanguard.

Gwamna Diri da Dockson.
Tsagin PDP sun matsawa gwamnan Bayelsa lamba kan Tinubu Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook

An matsawa Gwamna Diri kan Shugaba Tinubu

Sanata Dickson da Gwamna Diri dukkansu ’yan jam’iyyar PDP ne a halin yanzu kuma babu wata sahihiyar magana da ke nuna suna shirin komawa APC.

Sai dai wani tsagin PDP a jihar Bayelsa ƙarƙashin jagorancin George Turnah na matsa wa Gwamna Diri lamba da ya goyi bayan Shugaba Tinubu.

APC ta yi babban kamu a Bayelsa

A baya, kun ji cewa tsohon ɗan takarar gwamna na jam'iyyar LP kuma tsohon kwamishina a Bayelsa, Udengs Eradiri, ya sauya sheƙa zuwa APC.

Ya ce ayyukan alherin da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta yi wa al'ummarsa ne suka ja hankalinsa ya sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki.

Eradiri ya gode wa ƴaƴan APC a Bayelsa bisa kyakkyawar tarbar da suka masa, tare da alkawarin yin aiki da dukkan shugabannin jam’iyyar

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262