Ranar Ma'aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Hutun Kwana 1 a Najeriya

Ranar Ma'aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Hutun Kwana 1 a Najeriya

  • Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a, 1 ga watan Mayun 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin 'Ranar Ma’aikata ta Duniya' na shekarar 2026
  • Ministan cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, inda ya jinjina wa ma’aikatan Najeriya kan jajircewarsu wajen ciyar da ƙasa gaba
  • Gwamnati ta sake nanata ƙudurinta na inganta jin daɗin ma’aikata da samar da yanayi mai kyau domin bunƙasa kasuwanci da samar da ayyukan yi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a mai zuwa a matsayin ranar hutu domin girmama ma’aikatan ƙasar nan a bikin 'Ranar Ma’aikata ta Duniya' na shekarar 2026.

Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya taya daukacin ma’aikata murnar zagayowar wannan rana, yana mai bayyana su a matsayin kashin bayan ci gaban Najeriya.

Kara karanta wannan

NLC, TUC sun tsayar da lokacin tattauna sabon mafi ƙarancin albashi da gwamnatin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ayyana hutun kwana 1 don bikin ranar ma'aikata ta duniya.
Kashim Shettima ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a bikin ranar ma'aikata na shekarar 2025 a Abuja. Hoto: @stanleynkwocha
Source: Twitter

An ayyana ranar hutu a Najeriya

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu a ranar 29 ga watan Afrilun 2026, aka wallafa a shafin ma'aikatar na X.

A cikin sanarwar, ministan ya yaba wa ma’aikata kan yadda suke sadaukar da kansu wajen gudanar da ayyukansu duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

Sanatar ta nuna cewa ƙoƙarin ma’aikata shi ne sirrin dorewar zaman lafiya da wadata a ƙasar nan. Wani bangare na sanarwar ya ce:

"Gwamnatin tarayya ta ayyana Juma'a, 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin murnar bikin 'Ranar Ma'aikata ta Duniya.'
"Ministan cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya. Ya yaba wa ma'aikata bisa jajurcewarsu da sadaukar da kai wajen ci gaban kasa."

Alƙawarin inganta jin daɗin ma’aikata

Baya ga taya murna, Dr. Tunji-Ojo ya sake jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana iyaka ƙoƙarinta domin ganin an inganta walwala da tsaron ma’aikata.

Kara karanta wannan

"Umarnin jagora": Jigo a Kwankwasiyya ya fice daga jam'iyyar ADC a jihar Kano

Ya bayyana cewa samar da yanayi mai kyau ga ma’aikata shi ne zai ba su damar bayar da gudunmawa yadda ya kamata wajen gina ƙasa mai ƙarfi.

Ministan ya kuma yi kira ga daukacin ƴan Najeriya da su riƙa gudanar da ayyukansu cikin kishin ƙasa da kuma bin doka da oda a kowane lokaci.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya jinjinawa ma'aikata kan kokarin da suke yi wajen ci gaban Najeriya.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo a ofishinsa da ke Abuja. Hoto: @MinOfInteriorNG
Source: Twitter

Fatan ma'aikata kan sabon albashi

Ya buƙaci ma’aikata su yi amfani da wannan lokacin hutu domin yin tunani mai zurfi kan yadda za a ƙara haɗin kai da kuma himma wajen gina Najeriya wadda kowa zai yi alfahari da ita.

Wannan sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da ma’aikata ke fatan ganin an sake tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi domin rage raɗaɗin hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a faɗin ƙasar.

"Ya kamata a kara albashin ma'aikata" - Nura Maikarfe

A zantawar Legit Hausa da Nura Haruna Maikarfe, wani matashi a Katsina, ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta sake duba batun mafi karancin albashin ma'aikatan kasar.

"A halin da ake ciki, mafi karancin albashi na N70,000 ya yi kadan gaskiya. Lokacin da aka mayar da shi hakan nawa litar man fetur take? Yau kudinta ya nunka, ka ga idan adalci za a yi, to a ce mafi karancin albashin ya koma N140,000.

Kara karanta wannan

Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata

"Ba wai tarin kudi ne ke nuna daidaito ba, kamar yadda NLC ta fada, me kudin za su iya saya? Yau idan komai yana da sauki, ko N50,000 ake biyan ma'aikata babu laifi, saboda an san za ta ishi mai iyali gudanar da rayuwarsa har karshen watan ya yi."

- Nura Haruna Maikarfe.

Matashin ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta bullo da wani tsari da zai rage wa ma'aikata radadin matsin tattalin arziki da ake ciki.

NLC ta tabo batun sabon albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa ko da ma’aikata za su rika karbar albashin Naira miliyan daya, hakan ba zai amfane su ba.

Ajaero ya jaddada cewa hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa sun riga sun cinye karfin ikon sayayya na ma’aikata a Najeriya.

Game da sabon mafi karancin albashi, shugaban NLC ya ce tattaunawa za ta gudana ne bisa ka’idojin doka, kuma ba za a gaggauta yin ta ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com