Tinubu Ya Tsige Saidu Mohammed daga Shugabancin NMDPRA, Ya Nada Sabon Shugaba
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Rabiu Abdullahi Umar a matsayin sabon shugaban hukumar kula da albarkatun man fetur ta NMDPRA
- Wannan ya biyo bayan tsige Saidu Mohammed daga muƙamin, matakin da fadar shugaban ƙasa ta ce an ɗauke shi domin ƙarfafa ayyukan hukumar
- Rabiu Umar ƙwararre ne mai gogewar aiki ta shekaru sama da 25 a fannonin makamashi, masana'antu, da samar da ababen more rayuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya nada Rabiu Abdullahi Umar a matsayin sabon shugaban hukumar kula da albarkatun man fetur ta NMDPRA.
Fadar shugaban kasa, ta bayyana cewa wannan naɗi na Rabiu Abdullahi Umar yana jiran amincewar majalisar dattawa.
Tinubu ya nada sabon shugaban NMDPRA
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar da sanarwar nadin a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu, 2026, a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya tuna da mutanen da hare hare suka shafa a Plateau, ya ba da tallafin kudi
Shugaba Tinubu ya amince da tsige tsohon shugaban hukumar, Saidu Mohammed, inda ya bayyana cewa hakan ya zama dole domin ƙarfafa ingancin tsarin kula da fannin man fetur na tsakiya da na ƙasa, daidai da manufofin "Renewed Hope Agenda".
Sanarwar Onanuga ta ce:
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da tsige Saidu Mohammed daga mukamin shugaban hukumar NMDPRA. Shugaban ya kuma amince da nadin Rabiu Abdullahi Umar a matsayin sabon shugaban hukumar.
"Majalisar dattawa ce za ta tantace tare da tabbatar da nadin."
Kafin majalisar dattawa ta tantance Umar, babban jami’i mafi girma a hukumar ne zai riƙe ragamar gudanarwa na ɗan lokaci.
Wanene Rabiu Abdullahi Umar?
Rabiu Umar kwararren masani ne wanda ya gina suna a manyan kamfanoni na duniya da na gida, kamar yadda rahoton Business Day ya nuna.
Ya kammala karatunsa na digiri a fannin Akanta daga Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), sannan kuma tsohon ɗalibi ne a makarantar kasuwanci ta Harvard. Har ila yau, mamba ne a majalisar daraktoci.
Tarihin aikinsa ya haɗa da:
- Oando Plc: A nan ya fara aikinsa, inda ya riƙe muƙamai daban-daban a sashen tallace-tallace har ya kai ga jagorantar shirin sauya fasalin tallace-tallace na kamfanin.
- Lafarge Africa Plc: A shekarar 2014, ya zama daraktan makamashi da wutar lantarki, sannan ya kula da dabarun bunƙasa kasuwanci a ƙasashen yammacin Afirka kamar su Ghana da Kamaru.
- Ashaka Cement Plc: Ya kasance babban jami’in gudanarwa na kamfanin a shekarar 2016, inda ya yi garambawul ga kamfanin kafin ya bar aiki a 2019.
- Dangote Group: Kafin wannan naɗin, shi ne babban jami’in kasuwanci na rukunin kamfanonin Dangote.
Manufar wannan sauyi
Fadar shugaban ƙasa ta jaddada cewa wannan naɗi an yi shi ne bisa dogaro da dokar masana'antar man fetur ta 2021 (PIA).
Shugaba Tinubu ya gode wa tsohon shugaban hukumar, Saidu Mohammed, bisa gudunmawar da ya bayar, yana mai yi masa fatan alheri a ayyukansa na gaba.
Asali: Legit.ng
