2027: Yadda aka Fara Nemawa Tinubu Goyon Bayan Manyan Sarakunan Gargajiya
- Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya roƙi sarakunan Kudu maso Kudu da su mara wa shugaba Bola Tinubu baya ya zarce a 2027
- Ya bayyana cewa babu ci gaban da za a samu ba tare da goyon bayan sarakunan gargajiya ba, musamman wajen yaƙi da rashin tsaro da bunƙasa tattalin arziki
- Gwamnan ya ce Tinubu ya ɗauki matakai masu ƙarfi don dakile asarar kuɗin gwamnati da ƙarfafa ayyukan raya jihohi da ƙasa baki ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya nemi haɗin gwiwar sarakunan gargajiya a yankin Kudu maso Kudu domin ganin an sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin wakilan sarakunan a fadar gwamnatin jihar Edo da ke birnin Benin.

Asali: Twitter
Legit Hausa ta tattaro bayanan da gwamnan Edo ya yi ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafinsa na X
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya jaddada cewa goyon bayan sarakunan gargajiya yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da ci gaban Najeriya da nasarar manufofin gwamnatin Tinubu.
Gwamnan Edo ya roki sarakuna su zabi Tinubu
Gwamna Okpebholo ya ce lokaci ya yi da yankin Kudu maso Kudu zai fito da murya ɗaya wajen mara wa Tinubu baya domin ya kammala wa’adinsa na biyu.
The Guardian ta rahoto cewa gwamnan ya ce:
“Ya kamata mu mara masa baya.Tinubu ya ɗauki matakai da dama domin inganta tattalin arzikin ƙasa da kare albarkatun ƙasa daga salwanta.”
Ya kuma bayyana cewa ƙudirin Tinubu na haɓaka kuɗin shiga ta hanyar sauya tsarin haraji na daga cikin manyan matakan da za su taimaka wajen raya ƙasa.
Matsayin sarakuna a cigaban ƙasa
A cewarsa, sarakunan gargajiya suna da muhimmin matsayi a al’umma domin suna kusa da jama’a kuma sun fi sanin matsalolin da suke addabar ƙauyuka da unguwanni.
Ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da mutunta su tare da tabbatar da cewa gwamnonin yankin Kudu suna girmama su yadda ya kamata.
Gwamnan ya ce:
“Zan fara tattaunawa da sauran gwamnonin Kudu domin tabbatar da cewa ana ci gaba da mutunta masarautu da yadda suke taka rawa wajen zaman lafiya da ci gaba,”
Kokarin Tinubu na magance matsaloli
Gwamnan ya kuma amince cewa kasar nan na fama da ƙalubale da dama, amma ya bayyana cewa Shugaba Tinubu na yin iya ƙoƙarinsa wajen shawo kan su.

Asali: Facebook
Ya nemi sarakunan da su cigaba da ba da gudunmawa wajen ganin Najeriya ta fita daga matsalolin rashin tsaro da ƙuncin tattalin arziki.
Wike ya ce Tinubu zai ci zabe a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai lashe zabe a 2027.
Ministan ya bayyana haka ne bayan wani taron jam'iyyar PDP da aka gabatar domin warware rikicin jam'iyyar.
Wasu rahotanni sun nuna cewa Nyesom Wike ya gargadi PDP kan maganar fitar da dan takara daga yankin Arewa a zabe mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng