Shaidan Sojoji Ya Fasa Kwai a Kotu, Ya Fadi Yadda Aka Shirya Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

Shaidan Sojoji Ya Fasa Kwai a Kotu, Ya Fadi Yadda Aka Shirya Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

  • Rundunar sojin Najeriya ta yi bayanin yadda aka gano shirin kifar da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayin gabatar da shaida a kotu
  • Wani soja daga rundunar ‘yan sandan sojoji (NACMP), wanda kotu ta boye sunansa, ya bayar da shaida a shari'ar mutane shida da ake zargi
  • Binciken ya kuma gano wani kamfani mai suna Purple Wave wanda ake zargin an yi amfani da shi wajen daukar nauyin shirin juyin mulkin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa an yi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta hanyar juyin mulki.

Wani soja daga rundunar ‘yan sandan sojoji (NACMP), wanda kotu ta boye sunansa, ya bayar da shaida a kan mutane shida da ake zargi da shirya juyin mulkin.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta ba Tinubu damar ciyo bashin Dala miliyan 516 daga kasar waje

Kotu.
Kofar shiga babbar kotun tarayya mai zama a Abuja Hoto: Federal High Court
Source: Getty Images

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wadanda ake zargin sun hada da Manjo Janar Mohammed Ibrahim Gana (mai ritaya), Kyaftin Erasmus Ochegobia Victor (mai ritaya), Sufeto na ‘yan sanda Ahmed Ibrahim, da wasu mutum uku.

Haka zalika, an ambaci sunan tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, wanda kuma ya rike mukamin karamin Ministan Albarkatun Man Fetur a zamanin mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, watau Timipre Sylva.

Yadda aka gano shirin juyin mulki

Shaidan ya ce binciken ya fara ne bayan rahoton sirri da tsohon shugaban rundunar soji, Janar O. O. Oluyede, ya samu kan wani shiri na kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

Ya ce an kama Kanal M. A. Ma’aji, inda aka kwace wayarsa da wasu kayayyaki, haka kuma an gano wani littafi dauke da bayanai masu muhimmanci game da tuggun da suke shiryawa.

Abubuwan da sojoji suka gano

A cewarsa, littafin ya kunshi tsare-tsaren juyin mulki, sunayen manyan jami’ai da za a kashe, da sauye-sauyen siyasa da za a yi bayan nasarar juyin mulkin.

Kara karanta wannan

An fitar da hotunan bindigogi da wukaken da aka so kashe Trump da su

An kuma ce binciken fasaha da aka yi wa wayar ya nuna cikakken shirin juyin mulkin da ya hada da wasu jami’an soja da fararen hula, kamat yadda Leadership ta kawo.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Shaidan ya ce sun gano cewa an yi mu'amala ta kudade tsakanin Kanal Ma’aji, Timipre Sylva da wasu daga cikin wadanda ake tuhuma.

Ya ce an biya wasu kudade domin aiwatar da shirin, inda binciken ya kuma gano wani kamfani mai suna Purple Wave wanda ake zargin an yi amfani da shi wajen daukar nauyin shirin juyin mulkin.

Juyin mulki: Za a gurfanar da sojoji 36

A wani rahoton, kun ji cewa aƙalla jami'an sojoji 36 waɗanda ake zargi da yunkurin juyin mulki ga Shugaba Bola Tinubu ne za a gurfanar a gaban kotun soja.

Waɗanda za a gurfanar ɗin a gaban kotu suna cikin babban rukunin jami'an da ake tsare da su tun shekarar 2025 sakamakon zargin yunkurin juyin mulki.

Bugu da ƙari, an tabbatar da cewa duka masu ƙara da bangaren masu kariya za a ba su damar gabatar da shaidu daidai da tanadin dokar ba da shaida ta 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262