Sarki Sanusi II zai Yi Gagarumin Bikin Nadin Sarauta a Kano
- Masarautar Kano karkashin Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II za ta yi biki nadin sarauta ga wasu hakimai da aka karawa matsayi
- Rahotanni sun nuna cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II ya amince da sauye-sauye da suka shafi wasu masu rike da sarauta
- Wata takarda da Danmakwayon Kano, Alhaji Abba Yusuf ya sanya wa hannu ta nuna cewa Sarkin ya yi umarni da kowa ya hallara bikin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II ya sanar da wani shirin bikin sarauta da zai jagoranta a jihar Kano a makon nan.
A ranar 27 April, 2026 fadar mai martaba Khalifa Sanusi II ta sanar da cewa za a kara wa wasu masu rike da mukamai matsayi.

Source: Twitter
A wani sako da ya wallafa a Facebook, shafin Sanusi II Dynasty ya fitar da sunayen mutanen da za a karawa mukami a ranar da za a yi bikin, ciki har da hakimai da sauransu.
Muhammadu Sanusi II zai yi bikin nadin sarauta
Mai martaba Muhammadu Sanusi II zai jagoranci bikin karin matsayi ga wasu mutane 6 da suka hada da hakimai a jihar Kano a ranar Juma'a mai zuwa.
Rahotanni sun nuna cewa Danmakwayon Kano, Alhaji Abba Yusuf ya ce Hakiman Mariri da Garko na cikin wadanda za a ba karin sarauta.
Sanarwar da Danmakwayon ya fitar ta ce:
"Bayan gaisuwa da fatan alheri, an umarce ni da na sanar da ku cewa mai martaba, Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, PhD, CON, zai ciyar da wasu hakimai gaba a sarauta."
Hakiman Kano da za a karawa matsayi
Masarautar Kano ta ambaci mutane shida da za a karawa matsayi, inda za a gudanar da bikin nada su a jihar a karshen wannan makon:

Kara karanta wannan
Mutanen jihar Kano na cikin alheri a mulkin Tinubu, an raba wa talakawa Naira biliyan 48
1. Alhaji Aliyu Muhammad Wudil, Hakimin Garko
Daga Dokajin Kano zuwa Sarkin Sudan
2. Alhaji Mujtaba Abba, Hakimin Darmanawa
Daga Sarkin Yakin Kano zuwa Dokajin Kano
3. Amb. Ahmed Umar, Hakimin Mariri
Daga Jarman Kano zuwa Sarkin Yakin Kano
4. Alhaji Jafar Khalil Muhammad
Daga Ajiya Kano zuwa Jarman Kano
5. Alhaji Shafi Ahmad
Daga Kachallan Kano zuwa Talban Kano
6. Alhaji Sanusi Bello
Daga Barwan Kano zuwa Ajiyan Kano

Source: Twitter
Lokaci da ranar nadin sarautar
Masarautar Kano ta sanar da cewa za a yi bikin nadin sarautar ne a jihar kamar yadda mai martaba Muhammadu Sanusi II ya tsara:
Rana: Juma’a 1 ga Mayu, 2026
Lokaci: Karfe 9:00 na safe
Wuri: Kofar Kudu, Gidan Sarkin Kano
Sanarwar ta kara da cewa:
"Dan haka ake umartar ku da ku halarci nadin sarautu da za a yi a wannan rana idan Allah Ya kaimu.
"Allah Ya bamu lafiya da zaman lafiya, Amin."
Sanusi II ya caccaki Bola Tinubu
A wani labarin, mun kawo muku cewa Khalifa Muhammadu Sanusi II ya caccaki salon mulkin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Sarkin ya yi korafi game da yadda Bola Tinubu ke kara ciwo bashi duk da ya cire tallafin man fetur tun bayan zuwan shi mulki a 2023.
Mai martaban ya nuna cewa bai kamata a cigaba da ciwo bashi ba, ya ce ya kamata a yi aiki da kudin da aka samu domin ayyuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

