Tsohon Gwamnan PDP Ya Gano Abin da Zai Hana Jam'iyyar Rugujewa kafin 2027

Tsohon Gwamnan PDP Ya Gano Abin da Zai Hana Jam'iyyar Rugujewa kafin 2027

  • Tsohon gwamnan jihae Benue ya nuna damuwa kan rikicin da ya ƙi ci ya ƙi ci cinyewa na jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
  • Gabriel Suswam ya yi gargaɗin cewa idan shugabannin PDP ba su tashi tsaye ba, za ta iya rugujewa kafin nan da zaɓen shekarar 2027
  • Tsohon gwamnan ya nuna cewa PDP a halin yanzu tana a gaɓar ko dai ta tsira ne ko kuma a shafe tarihinta gaba ɗaya a doron ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam, ya yi gargaɗin cewa jam’iyyar PDP na iya rugujewa kafin zaɓen 2027.

Gabriel Suswam ya bayyana cewa PDP za ta ruguje ne idan shugabannin jam’iyyar ba su ɗauki matakan gaggawa don gyara matsalolinta ba.

Gabriel Suswam ya tabo batun rikicin PDP
Gabriel Suswam ya ce PDP za ta iya rugujewa kafin 2027 Hoto: Gabriel Suswam, Official Peoples Democratic Party
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na Benue ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise Tv a shirinsu na 'The Morning Show' a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin yanzu, jam'iyyar PDP na fama da rikici dangane da wanda zai zama sakataren jam’iyyar na ƙasa.

Haka zalika, jam’iyyar ta fuskanci matsalar ficewar manyan ƴaƴanta, ciki har da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da wanda ya gabace shi, Sanata Ifeanyi Okowa, da wasu tsofaffin shugabanni da mambobin jam’iyyar zuwa APC.

Gabriel Suswam ya ce PDP na cikin matsala

Gabriel Suswam ya bayyana cewa jam’iyyar PDP na cikin wani hali na tsaka mai wuya.

“Mutane da dama sun tsaya ne kawai suna jiran su ga yadda za ta ƙare da jam’iyyar.”

- Gabriel Suswam

Ya bayyana cewa yawancin mambobin jam’iyyar sun rasa ƙwarin gwiwa, suna ganin PDP ba za ta iya kai labari ba.

Wace hanya za a iya ceto PDP?

Suswam ya ce ƙoƙarin da gwamnoni da tsofaffin gwamnoni na PDP ke yi, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, na iya taimakawa wajen ceto jam’iyyar.

Gabriel Suswam
Suswam ya ce PDP na cikin tsaka mai wuya Hoto: Gabriel Suswam
Asali: Facebook
“Ko akwai alamun nasara a ƙoƙarin da Sanata Saraki ke yi? Za mu gani cikin makonni biyu masu zuwa. Amma a yanzu, zan ce shin PDP tana cikin asibiti? Eh. Shin tana cikin ɗakin kulawa ta musamman (ICU)? A wani ɓangare, eh. Za a iya ceto ta? Eh, idan aka ba ta maganin da ya dace."

- Gabriel Suswam

Ya ƙara da cewa, kwatanta PDP da mara lafiya a ICU na nufin rabi da rabi ne tsakanin tsira ko mutuwa.

Tsohon gwamnan ya yi gargaɗin cewa idan ƙoƙarin da tawagar Saraki ke yi ya ci tura, jam’iyyar PDP ba za ta tsira ba.

Sanatocin PDP sun koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatocin jam'iyyar PDP daga jihar Kebbi sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Sanatocon guda uku sun tabbatar da ficewarsu daga PDP ne a hukumance cikin wata wasiƙa da suka aikawa majalisar dattawa.

Komawarsu APC na zuwa ne bayan a makon da ya gabata sun sanya labule da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng