"Tinubu Ya Fi El Rufai Farin Jini a Kaduna", Gwamna Sule Ya Fadi Dalili

"Tinubu Ya Fi El Rufai Farin Jini a Kaduna", Gwamna Sule Ya Fadi Dalili

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi wa Nasir El-Rufai martani kan kalaman da ya yi kan Shugaba Bola Tinubu
  • Abdullahi Sule ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya fi samun goyon baya a yanzu a Kaduna fiye da lokacin da El-Rufai ke gwamna
  • Gwamnan ya ba da misali da yadda tsohon gwamnan na Kaduna ya kasa kawo jihar ga Tinubu a zaɓen shekarar 2023

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya kwatanta goyon bayan da Shugaba Bola Tinubu ya samu yanzu a Kaduna da lokacin mulkin Nasir El-Rufai.

Gwamna Sule ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya fi samun goyon baya a jihar Kaduna a yanzu fiye da yadda ya samu a shekarar 2023 lokacin da tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ke kan mulki.

Abdullahi Sule, Bola Tinubu
Gwamna Sule ya kare Bola Tinubu Hoto: Abdullahi A. Sule, Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a tashar TVC News da yammacin ranar Talata, 14 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sule ya yi wa El-Rufai martani

Gwamna Sule ya ƙi yarda da wasu kalaman da El-Rufai ya yi kwanan nan, inda ya nuna cewa farin jinin Shugaba Tinubu a Arewacin Najeriya yana raguwa.

Abdullahi Sule ya ce gaskiyar yadda al'amura suke a yanzu ya nuna saɓanin abin da tsohon gwamnan ya ce.

“Shugaba Tinubu yana da goyon baya a yanzu a jihar Kaduna wadda El-Rufai ya fito daga cikinta fiye da wanda ya samu a lokacin da El-Rufai ke gwamna."
"Ai ko lokacin da El-Rufai ke gwamna, Tinubu bai samu fiye da ƙuri’u 300, 000 da wani abu ba, ya sha kaye a Kaduna a wancan lokacin."

- Gwamna Abdullahi Sule

Gwamna Sule yace Tinubu na samun goyon baya

Gwamnan ya ƙara da cewa, ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Uba Sani a yanzu, ra’ayoyin jama’a game da Shugaba Tinubu sun inganta ƙwarai, musamman a yankin Kudancin Kaduna.

“Idan ka kalli Kudancin Kaduna, har ma da ƙaramar hukumar da na fito daga cikinta a Nasarawa, wadda ke iyaka da wasu sassan Kaduna, ina jin abin da jama’a ke cewa game da Shugaba Tinubu a yau."
"Goyon bayan da yake samu ya fi ƙarfi yanzu ƙarƙashin Gwamna Uba Sani fiye da lokacin El-Rufai."

- Gwamna Abdullahi Sule

Abdullahi Sule
Gwamna Sule ya yi wa El-Rufai martani Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Gwamna Sule, wanda babban jigo ne a jam’iyyar APC, ya kuma taɓo batun yaɗa bayanan da ba su da tushe a siyasa, ya gargadi jama’a da su guji yarda da kowane zance da suka ji ana yaɗawa.

"Ƴan siyasa na iya cewa duk abin da suka ga dama. Amma gaskiyar magana ita ce, a yau Shugaba Tinubu yana da goyon baya sosai a Kaduna fiye da shekarar 2023, lokacin da ya sha kaye da fiye da ƙuri’u 300, 000 a hannun PDP."

- Gwamna Abdullahi Sule

Ƴan APC sun taso Gwamna Sule a gaba

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiyar jam'iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiya ta taso Gwamna Abdullahi Sule a gaba.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ba ta ji daɗin kalaman da gwamnan ya yi ba kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban ƙungiyar, Saleh Mamman Zazzaga ya buƙaci gwamnan da ya fito fili ya bayyana yana tare da Shugaba Tinubu ko kuma akasin haka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng