Jam'iyyar PDP Ta Yi Martani kan Ficewar Sanatocinta 3 zuwa APC

Jam'iyyar PDP Ta Yi Martani kan Ficewar Sanatocinta 3 zuwa APC

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeryia ta yi magana kan ficewar wasu sanatocinta guda uku daga jihar Kebbi zuwa APC
  • Shugaban PDP na jihar Kebbi ya bayyana cewa ficewar sanatocin ba zai rage tasiri ko ƙarfin da jam'iyyar take da shi ba
  • Usman Bello Suru ya zargi sanaatocin da zama butulu bayan da PDP ta ba su mafaka a lokacin da APC ta kore su a baya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Kebbi ta yi martani kan ficewar sanatocinta uku zuwa APC.

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa ficewar sanatocin guda uku zuwa APC ba zai rage ƙarfin ta ko tasirin ta ta a jihar ba.

Sanatocin PDP a Kebbi
Jam'iyyar PDP ta ce ba ta damu da ficewar sanatocinta zuwa APC ba Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kebbi, Usman Bello Suru ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyarta da ke Birnin Kebbi, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatocin PDP sun tsallaka zuwa APC

A ranar Talata, majalisar dattawa ta tabbatar da sauya shekar Sanata Adamu Aliero mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Yahaya Abdullahi daga Kebbi ta Arewa, da kuma Garba Maidoki daga Kebbi ta Kudu, daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

An sanar da sauya sheƙar tasu a hukumance yayin zaman majalisar dattawa a ranar Talata, bayan sun yi murabus daga PDP a kwanakin baya.

Sauya sheƙar tasu a hukumance ta zo ne kwanaki kaɗan bayan sun bayyana shiga jam’iyya mai mulki, bayan wata ganawa da shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Wane martani jam'iyyar PDP ta yi?

Shugaban na jam'iyyar PDP ya bayyana matakin da sanatocin suka ɗauka a matsayin cin amanar jam’iyya.

“Muna da ƙwarin gwiwa duk da sauya sheƙar da suka yi. PDP na nan daram kuma za ta ci gaba da kasancewa da ƙarfi a jihar Kebbi."

- Usman Bello Suru

Ya nuna rashin jin dadinsa, yana mai cewa jam’iyyar ce ta tallafawa sanatocin lokacin da APC ta hana su tikitin takara a zaɓen 2023.

"Lokacin da APC ta yi watsi da su, PDP ce ta basu dama kuma ta tsaya tare da su. Yanzu kuma sun koma APC ɗin da ta jefa al’umma cikin halin ƙunci da tsadar rayuwa."

- Usman Bello Suru

Jam'iyyar PDP
Jam'iyyar PDP ta ce sanatocin da suka koma APC sun yi mata butulci Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Shugaban na PDP ya soki dalilan sauya sheƙar nasu, yana mai cewa buƙatun kansu ne suka ja hankalinsu, ba buƙatun jama’a ba.

“Ba don jama’a suka bar PDP ba. Sun bar jam’iyyar ne saboda son zuciyarsu. Wannan rashin godiya ne."

- Usman Bello Suru

Gabriel Suswam ya magantu kan rikicin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, ya nuna damuwa kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP.

Gabriel Suswam ya bayyana cewa idan shugabannin PDP ba su tashi tsaye ba, jam'iyyar na iya rugujewa kafin nan da zaɓen shekarar 2027.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa PDP na cikin halin tsaka mai wuya na a mutu ko a yi rai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng