Bayan Kisan Ministan Tsaro, Shugaban Mali Ya Magantu kan Zargin Juyin Mulki

Bayan Kisan Ministan Tsaro, Shugaban Mali Ya Magantu kan Zargin Juyin Mulki

  • Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Mali, Assimi Goita, ya yi magana bayan harin yan ta'adda wanda ya yi ajalin ministan tsaro
  • Goita ya tabbabar cewa gwamnati na kokarin kan lamarin bayan hare-haren da suka hallaka jama'a tare da jikkata mutane da dama
  • Kungiyoyin masu ikirarin jihadi masu alaƙa da Al Qaeda sun kai hare-hare a sansanonin soji da kusa da filin jirgin Bamako

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bamako, Mali - Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Mali, Assimi Goita, ya yi magana a karon farko bayan kashe ministan tsaro.

Goita ya bayyana cewa halin da ake ciki yana ƙarƙashin iko bayan hare-haren da masu tayar da ƙayar baya suka kai a ƙarshen mako.

Shugaban Mali ya magantu bayan kisan ministan tsaro
Shugaban kasar Mali, Assimi Goita yana jawabi a taro. Hoto: MALIK KONATE.
Source: Getty Images

Shugaban Mali ya sha alwashi kan ta'addanci

Goita ya bayyana hakan ne a wani jawabi da aka watsa a talabijin inda ya sha alwashin “murƙushe” waɗanda suka kai hare-haren, cewar Reuters.

Kara karanta wannan

Yana ajiye mukamin minista, Tuggar ya fadi abin da ya jawo ta'addanci a Bauchi

Kungiyoyin masu alaƙa da Al Qaeda da kuma wasu ‘yan tawaye ‘yan Tuareg sun kai hare-hare kan babban sansanin sojin Mali da yankin kusa da filin jirgin Bamako ranar Asabar.

Hare-haren sun kuma tilasta wa sojojin Rasha da ke taimaka wa gwamnatin Mali janyewa daga garin Kidal mai muhimmanci da ke arewacin ƙasar.

Rahotanni sun bayyana cewa hare-haren sun janyo sabon rikici a hamadar Arewacin Mali, inda kungiyoyin masu dauke da makamai ke ƙoƙarin kwace yankuna masu yawa.

Yan ta'adda sun kashe ministan tsaron Mali
Ministan tsaron kasar Mali, Sadio Camara yayin taro a Bamako. Hoto: FANNY NOARO-KABRE/AFP.
Source: Getty Images

Tsaron Mali: Rasha ta tsoma baki

An kuma tabbatar da mutuwar ministan tsaron Mali, Sadio Camara, a yayin hare-haren da aka kai ranar Asabar 26 ga watan Afrilun 2026.

Bayan faruwar lamarin, fadar shugaban ƙasa ta wallafa hotunan Goita yayin ganawarsa da jakadan Rasha, Igor Gromyko, a Bamako.

Jakadan ya sake tabbatar da cewa Rasha za ta ci gaba da tallafawa Mali wajen yaƙi da abin da ya kira ta’addancin ƙasa da ƙasa.

Majiyar Channels TV sun bayyana cewa an ji karar harbe-harbe a wasu yankuna daban-daban na ƙasar Mali da ke ƙarƙashin mulkin soja.

Cikin garuruwan da aka kai hari har da Kati, mahaifar shugaban mulkin soja Janar Assimi Goita da ake zargin akwai shirin juyin mulki.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi ta'asa, sun hallaka ministan tsaron Mali yayin hari a gidansa

Daga baya, Goita ya kai ziyara asibitin da ake kula da waɗanda suka jikkata a hare-haren tare da jajanta wa iyalan ministan tsaron da ya rasu.

A wani saƙon bidiyo, mai magana da yawun ƙungiyar JNIM mai alaƙa da Al Qaeda, Bina Diarra, ya yi barazanar killace Bamako gaba ɗaya.

A nata ɓangaren, Rasha ta ce mayaƙan masu tayar da ƙayar baya suna sake haɗa ƙarfi bayan dakile wani yunƙurin juyin mulki da suka ce an yi ranar Asabar.

Mali, Burkina Faso sun yi barazana ga Najeriya

Mun ba ku labarin cewa rahotanni sun nuna cewa kungiyar AES ta ba da umarni cewa a harbo duk wani jirgin da ya keta sararin samaniyar mambobinta.

Umarnin ya biyo bayan zargin cewa jirgin saman sojojin Najeriya ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izini ba.

Shugaban kasar Mali, Asimi Goita ya ce shiga yankinsu ba tare da izini ba rashin mutuntawa ne ga dokokin ƙasa da ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.