"Tauraruwarsa Ta Daina Haskawa," Hadimin Tinubu Ya ce Siyasar El Rufa'i Ta Mutu
- Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya ce farin jinin tsohon gwamna, Nasir El-Rufa'i ya yi kasa sosai, wanda ya jawo wa APC matsala a baya
- Ya kuma caccaki hadakar adawar Atiku Abubakar da El-Rufa'i, ya ce ta ki samun karbuwa ne saboda rashin alaka da talaka da sauran yan kasa'
- Bwala ya kuma yi magana a kan maido mulkin kasar nan ga yankin Arewa, yana mai cewa 'yan Kudu na da yancin dansu ya yi shekara takwas a mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hadimin musamman na shugaban kasa Bola Tinubu kan harkokin yada labarai, Daniel Bwala, ya yi magana kan siyasar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i.
Bwala ya ce wannan hadakar adawa da ya aka kafa da El-Rufa'i ba ta da tasiri ko kadan, wanda ya alakanta da rashin sahihiyar alaka da talakawa.

Asali: Facebook
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Bwala ya ce akwai kuskure a yadda ake kallon siyasar Arewa, inda a kan dauki wasu kalilan daga cikin manyan mutane a matsayin wakilan Arewa yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Arewa ba za ta zabi danta ba,’ in ji Bwala
Jaridar The Cable ta ruwaito Bwala ya ce yana sane da yadda jama’ar Kudu ke ganin yadda Arewa ta yi shekara takwas a mulki, ya kamata yanzu a bar dan yankinsu ya yi shekara takwas.
Bwala ya ce:
“Wadannan mutanen Kudu da ke da wannan ra’ayi, su ma suna cikin jam’iyyun da ’yan Arewa suka tsaya takara. Amma ba za su kada wa dan Arewa ba kuri'a ba, sai dai dan Kudu. Kuma hakan adalci ne, daidai ne, kuma ya dace.”
‘Siyasar El-Rufa'i ta mutu,’ in ji Bwala
A cewar Bwala, siyasar El-Rufai ta fara dusashewa tun kafin ya bar mulki. Ya ce rashin karbuwa da jam’iyyar APC ta fuskanta a zaben zabukan 2019 a Kaduna na nuna irin dushashewarsa.

Asali: UGC
Bwala ya ce:
“Masu nazarin siyasa suna kallon alkaluma da kididdiga. A lokacin wa’adin mulkinsa na biyu, ya zama ba shi da farin jini har jam’iyyar APC ta rasa kujeru uku na sanata, da dama a Majalisar Wakilai, har ma shugaban kasa ya sha kaye a jihar.”
“Wasu ba za su kalli irin wadannan abubuwa ba, amma masu nazarin siyasa suna kallonsu a matsayin alamun karfin siyasa."
Bwala ya kara da cewa a cikin wannan hadakar da ake kokarin ginawa, ana ta kokarin shawo kan El-Rufai ya PDP yar bar SDP da ya koma a kwanan nan.
Bwala ya yiwa Atiku shugube
A wani labarin, mun wallafa cewa hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala, ya ce babu wata garumar haɗakar jam’iyyun adawa da ke shirin fuskantar APC a zaɓen 2027 mai zuwa.
Bwala ya karyata cewa jam’iyyun adawa na ƙara haɗa kai, yana mai cewa babu wata jam’iyya ko ɗan siyasa da ya fito fili ya mara wa hadakar Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai baya.
Bwala, wanda tsohon na hannun daman Atiku Abubakar ne kafin ya sauya sheƙa zuwa APC, ya caccaki tsohon ubangidansa, yana mai cewa kowa na gudun hadakar da yake jagoranta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng