Rikicin PDP
Edision Ehie, ya yi murabus daga kujerar shugaban tsagi ɗaya na majalisar dokokin jihar Ribas, ya kuma aje kujerar mamba mai wakiltar mazaɓar Ahaoda ta gabas.
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya ziyarci tsohon gwamna Ayodele Fayose na Ekiti a gidansa da ke Lagas. An bayyana cikakken bayanin ganawar tasu.
Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ta jaddada cewa ba gudu ba ja da baya dukkan yan majalisar jihar Ribas da suka sauya sheƙa zuwa APC sun rasa kujerunsu.
Babbar jam'iyyar adawa ta ƙara shiga sabon kace-nace bayan tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya tsoma baki a rikicin siyasar jihar Ribas wanda aka warware.
Babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa ta fara cike guraben da ta rasa a kwamitin gudanarwa na jihar Imo wata ɗaya bayan kammala zaben gwamnan da aka yi a Nuwamba.
Tsohon kwamishinan PDP, David Briggs ya fito ya yi magana da manema labarai a game da rikici da sulhun da aka yi wa Nyesom Wike da Simi Fubara ta hannun Bola Tinubu.
An fara taso Shugabannin PDP a gaba saboda sun gagara ladabtar da Nyesom Wike. Sule Lamido ya yi Allah-wadai da yadda abubuwa su ke tafiya a jam’iyyarsa ta PDP.
Bola Ahmed Tinubu ya yi zama da kusoshin siyasar Ribas domin a birne sabanin da ya jawo rikici. Mun tattaro jerin mutum 10 da aka yi taron sulhu da su a Aso Villa
Mambobin majalisar dokokin jihar Ribas sun janye sanarwan fara shirin tsige wa da suka tura wa Gwamna Siminalayi Fubara a zamansu na farko ranar Laraba.
Rikicin PDP
Samu kari