Rigima ta ɓalle, Mataimaki Shaibu Ya Fara Caccakar Gwamnan PDP Kan Zaben Jihar Na 2024

Rigima ta ɓalle, Mataimaki Shaibu Ya Fara Caccakar Gwamnan PDP Kan Zaben Jihar Na 2024

  • Mataimakin gwamnan Edo ya ce babu tantama zai lallasa duk ɗan takarar da Gwamna Godwin Obaseki yake goyon baya a PDP
  • Philip Shaibu, ya bayyana cewa mutanen jihar Edo suna buƙatar nasu ba wanda aka kakaba musu da karfin tsiya ba
  • Wannan kalamai na zuwa ne kwana ɗaya bayan Shaibu ya ayyana shiga neman takarar gwamnan jihar Edo a zaɓe mai zuwa 2024

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya bayyana kwarin guiwar samun nasara a zaɓen gwamnan jihar mai zuwa a shekarar 2024.

Mista Shaibu ya ce babu tantama zai doke duk ɗan takarar da gwamnan jihar mai ci, Godwin Obaseki, ya tsaida a zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ake shirin tsige Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu.
Zaben Edo: "Zan tumurmusa duk ɗan takarar da Obaseki ya tsayar" Shaibu Hoto: Philip Shaibu
Asali: UGC

Mataimakin gwamnan ya yi wannan furucin ne a cikin wata hira da ya halarta a cikin shirin TVC da yammacin ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne awanni 24 bayan ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Edo.

Bayan bayyana kudirinsa na neman tikitin PDP, Shaibu ya kaddamar da ofishin yaƙin neman zabensa a Benin City, babban birnin jihar.

Taron buɗe ofishin kamfen ɗin mataimakin gwamnan ya ja hankali ganin yadda magoya bayan PDP suka yi tururuwa a wurin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ni mutane suke so a Edo - Philip Shaibu

Shaibu ya ce:

"Babu shakka zan lallasa kowaye wanda gwamna ya tsaida, ba wai don ina kan madafun iko ba, a'a saboda mutanen Edo suna ƙaunar na su kuma nine na su."

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan PDP ya daga wa mai gidansa yatsa, ya fito takarar gwamna a jihar

"Al'ummar jihar Edo ba su bukatar a musu ƙarfa-ƙarfa, suna tare da wanda suke kallo a matsayin na su. Matsalar da ta shiga tsakanina da gwamna ita ce ya bar wasu mutane masu kwaɗayin mulki sun shiga tsakanin mu."
"A yanzu ya koma yana tafiyar da harkokinsa da salo irin nasa, nima kuma ina nawa harkokin da salo irin nawa. Lokacin da na ce an danne ni, amma ban damu ba, na fahimci irin tursasawa da zaluncin da nake ciki."

Rigimar da ke tsakanin Obaseki da shaibu ta dawo sabuwa bayan mataimakin gwamnan ya tabbatar da shiga tseren takarar gwamna a inuwar PDP, jaridar Guardian ta rahoto.

Shugaba Tinubu Ya Sake Nada Mele Kyari

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake naɗa Malam Mele Kyari a matsayin shugaban kamfanin man fetur na ƙasa NNPCL

Shugaban ƙasar ya kuma naɗa majalisar gudanarwan kamfanin wadda ta ƙunshi Pius Akinyelure a matsayin shugaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel