Babban Malamin Addini Ya Bayyana Yadda PDP Za Ta Iya Kwace Mulki a Hannun APC

Babban Malamin Addini Ya Bayyana Yadda PDP Za Ta Iya Kwace Mulki a Hannun APC

  • Primate Elijah Ayodele ya ce jam'iyyar PDP za ta iya dawowa mulki ne kawai "idan suka cire batun rashin hadin kai" a tsakanin su
  • Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ya bayyana cewa akwai rashin haɗin kai da aka jefi jam'iyyar PDP da shi
  • Malamin ya yi gargaɗin cewa idan jam'iyyar PDP ta kasa shawo kan rikicin ta nan ba da daɗewa ba, to za ta iya faɗuwa a zaben shugaban ƙasa na 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Primate Babatunde Elijah Ayodele ya ce jam’iyyar PDP za ta iya zama jam’iyya mai mulki a Najeriya ne kawai idan ta warware rikicin cikin gida da take fama da shi.

Kara karanta wannan

Wasu manyan jiga-jigan NNPP sun shiga sabuwar matsala bayan hukuncin tsige Abba Gida-Gida

Primate Ayodele a wani saƙo na baya-bayan nan da ya sanya a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) ya nemi jam’iyyar PDP da ta haɗa kai.

Primate Ayodele ya yi magana kan rikicin PDP
Primate Ayodele ya shawarci PDP ta magance rikicin da ya addabe ta Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele, Nuru Shehu
Asali: Facebook

Ku sasanta rikicin ku, Ayodele ya shawarci PDP

Jam'iyyar PDP ta shafe shekara 16 tana mulkin Najeriya, kuma tun bayan da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta kori jam'iyyar a shekarar 2015, sau biyu ta yi yunƙurin korar APC amma ba ta yi nasara ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Primate Ayodele a saƙon nasa ya ce:

"Gaskiyar magana ita ce PDP za ta iya dawowa daidai ne kawai idan ta cire batun rashin haɗin kai. Akwai rashin haɗin kai da suka jefi jam'iyyar PDP da shi. Sai dai idan sun daidaita wannan rashin haɗin kai. Idan ba su daidaita wannan rashin haɗin kai ba, PDP ba za ta yi kyau ba. Zai sake ɗaukar su wani lokaci."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC mara lafiya ya kashe N7.3bn lokacin jinya? APC ta bayyana gaskiya

Rikicin PDP a Rivers Ya Ɗauki Sabon Salo

A wani labarin kuma, rikicin siyasar da ya kaure a tsakanin jiga-jigan jam'iyyar PDP a jihar Rivers ya ɗauki sabon salo.

Hakan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike ya zargi Gwamna Siminalayi Fubara da yi masa butulci bayan ya ɗare kan madafun ikon jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel