Asalin Abin da Ya Hada Ni Fada da Mai Girma Gwamna Inji Mataimakin Gwamnan Jihar Edo

Asalin Abin da Ya Hada Ni Fada da Mai Girma Gwamna Inji Mataimakin Gwamnan Jihar Edo

  • A yanzu mataimakin gwamna da mai gidansa watau Gwamna Mista Godwin Obaseki sun samu sabani a jihar Edo
  • Da aka yi hira da shi, Philip Shaibu ya fadi daga inda matsalar ta fito har ta nemi jawo baraka a gidan gwamnati
  • Shaibu ya ce yana so ya zama gwamnan Edo ne a 2024 shi kuma Obaseki wanda zai bar mulki bai goyon bayansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Edo - Philip Shaibu wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar Edo, ya bada dalilin rashin jituwar da ke tsakanin sa da Godwin Obaseki.

‘Dan siyasar ya shaidawa gidan talabijin saboda yana so ya gaji Mai girma gwamna, aka samu rashin jituwa tsakanin sa da Godwin Obaseki.

Mista Philip Shaibu wanda ya fito neman tikitin zama ‘dan takaran gwamna a PDP ya ce burin zama gwamna ne silar rikicin siyasar Edo.

Kara karanta wannan

Edo: Ubangiji ne ya umurce ni in nemi kujarar gwamna, In Ji Shaibu

Philip Shaibu
Mataimakin Gwamnan Edo Hoto: Rt. Hon. Comrade Philip Shaibu
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takarar Gwamna ta hada fada a Edo

A cewar shi, Godwin Obaseki yana da wani ‘dan takara dabam da ba shi ba, wanda yake so ya zama gwamna idan shi ya bar karagar mulki.

Shuaibu ya ce rikicin siyasar ya fara ne tun lokacin da ya taya Adams Oshiomhole murna sakamakon ya lashe zaben Sanata a jam’iyyar APC.

Tsohon gwamnan wanda ba a ga maciji da shi da Obaseki ya yi galaba a kan PDP mai mulkin Edo a kujerar Sanatan jihar Edo ta Arewa a 2023.

Alakar Adams Oshiomhole da Shaibu

"Daga cikin rigimar da na samu da Obaseki shi ne lokacin da na je Majalisar dattawa domin yi wa Adams Oshiomhole murna, sai na fito a bidiyo.
Tun daga nan matsalar ta fara domin a tsarin gwamnan, idan kai abokinsa ne, dole ka zama abokinsa, kuma ka zama makiyi na makiyinsa."

Kara karanta wannan

Rigima ta ɓalle, Mataimaki Shaibu ya ɗara caccakar Gwamnan PDP kan zaben jihar na 2024

- Philip Shaibu

Shaibu ya ce duk da ya na ta faman kaffa-kaffa wajen yi wa Adams Oshiomhole shisshigi, ya yi farin ciki da gwamna ya fara jawo Sanatan.

Kwanakin baya gwamnatin Edo ta gayyato Sanata Oshiomhole wanda Shaibu ya kira uba, Premium Times da ta kawo labarin ta tabbatar da haka.

Mista Shaibu yake cewa tun da Obaseki ya fara sasantawa da tsohon mai gidansa, kyau yanzu shi ya nemi afuwar kalaman da ya yi lokacin zabe.

Shaibu zai samu takaran gwamnan Edo a PDP?

Ina mai tabbatar maka zan samu tikiti kuma sunana zai kasance ya fito a takardar zabe.
Za a aika sunana zuwa INEC kuma zan zama ’dan takaran PDP a zaben domin ban yi abu sai na duba. Na zagaya kuma an tabbatar mani.”

- Philip Shaibu

Oshiomhole ya kai Gwamna Obaseki PDP

Adams Oshiomhole wanda ya taimaka wajen zaman Obaseki gwamna ya yi fada da shi daga fara mulki, rigimarsu ce ta jawo ya koma PDP.

A yanzu ana makamancin rikicin a PDP, Shaibu ya dage sai ya samu takaran gwamnan Edo ko da gwamna da ke kan mulki bai so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel