'Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun Bude wa Mutane Wuta a Wurin Jana'iza a Filato

'Yan Bindiga Sun Nuna Rashin Imani, Sun Bude wa Mutane Wuta a Wurin Jana'iza a Filato

  • 'Yan bindiga sun kai hari kan masu jana'izar gawarwakin da aka kashe a yankin karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar Filato
  • Majiyoyi sun ce maharan sun kai hare-hare kusan kauyuka biyar lokaci guda, kuma ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu
  • Sakataren kungiyar 'yan kabilar Berom, Rwang Tengwong ya bayyana lamarin a matsayin babban abin tashin hankali

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Filato, Nigeria - Ana fargabar mutane da dama sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan wasu ‘yan bindiga su! bude wuta a wurin jana'iza a jihar Filato.

Maharan sun aikata wannan danyen aiki ne a gundumar Nding Fan da ke karamar hukumar Barkin Ladi a jihar da ke Arewta Tsakiya a Najeriya.

Filato.
Taswirar jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yan bindiga sun farmaki wurin jana'iza

Jaridar Vanguard da tattaro cewa wadanda aka kai wa harin sun halarci jana’izar mutane bakwai da aka kashe a wani hari da aka kai wa al’ummar yankin tun da farko.

Kara karanta wannan

Daga rantsar da mataimakin gwamna, 'yan daba sun hallaka matasa 5 a Kano

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi yayin da mazauna kauyen suka taru domin gudanar da jana’izar.

An kuma tattaro cewa maharan, wadanda suka kasance suna bibiyar taron daga tsaunukan da ke kewaye da yankin, sun sauko ba zato ba tsammani suka fara harbe-harbe kan masu makoki yayin da suke tona kaburbura.

Mahara sun shiga kauyuka 5 a Filato

Wani shaidan gani da ido kuma dan jarida mai suna Masara Kim, ya shaida cewa kauyuka biyar ne suka fuskantar hare-hare a lokaci guda daga hannun ‘yan bindigar.

Ya ce masu jana’izar ba su gama tona kabari sosai ba lokacin da maharan suka fara kai hari kauyuka, lamarin da ya tilasta musu binne gawarwakin cikin gaggawa tare da tserewa domin tsira da rayukansu.

Masara Kim ya ce:

“Ana yawan kai munanan hare-hare a yankunan kudancin Jos, fiye da garuruwa biyar ne ake kai wa hari a lokaci guda. Yayin da muke wajen jana’izar, maharan sun fito daga tsaunuka suka fara harbe-harbe.”

Mutane nawa aka kashe a harin?

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An bindige mahaifin amarya ana tsaka da bikin auren 'yarsa

Ya kara da cewa an harbe wani mutum har lahira a gabansa, yana mai cewa masu kare yankin da bindigogin farauta da makaman gargajiya sun kasa dakile maharan.

Kim ya ce ya tsallake rijiya da baya, yana mai cewa mutane da dama sun tsere daga yankin yayin da maharan ke ci gaba da kutsa kai.

Mutumin ya kuma bayyana cewa a yanzu, ba zai iya tantance adadin wadanda suka mutu ba saboda rudanin da ya biyo bayan harin, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Gwamnan Filato.
Gwamna Caleb Mutfwang yayin wata ganawa a fadar gwamnatin jihar Filato da ke Jos Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Da aka tuntubi Sakataren Yada Labarai na kungiyar Berom Youth Moulders Association, Rwang Tengwong, ya bayyana lamarin a matsayin “abin tashin hankali,” yana mai cewa ana kokarin ceto mutanen da suka makale a yankin.

Yana bindiga sun kashe fasto a Filato

A baya, kun ji cewa 'yan bindigan sun kashe wani fasto da wasu daga cikin iyalinsa a yayin harin da suka kai a cikin dare a ƙauyen Gako da ke ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato.

Waɗanda maharan suka kashe sun hada da Fasto Ayuba Choji, matarsa Chundung Ayuba, da kuma yayansu biyu, Cyril Ayuba da Endurance Ayuba.

Wata mazauniyar yankin, Martha Dalyop, ta shaida wa manema labarai cewa ƙarar harbin bindigar ya tursasa wa mazauna garin gudu don tsira da rayukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262