Sabon Rikici Ya Kunno PDP Yayin da Atiku da Fitaccen Gwamna Suke Neman Iko, Karin Bayani

Sabon Rikici Ya Kunno PDP Yayin da Atiku da Fitaccen Gwamna Suke Neman Iko, Karin Bayani

  • Babu alama da ke nuna rikicin cikin gida da ya dabaibaye babbar jam'iyyar adawa ta PDP zai kare a yanzu
  • Wani sabon rahoto ya nuna cewa Atiku na fafutukar karbe ragamar iko a jam'iyyar bayan kayen da ya sha a zaben shugaban kasa na 2023
  • Atiku na ganin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, zai nemi takarar tikitin PDP a 2027, saboda haka, an fara fafatawa kenan

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zabukan 2019 da 2023, yana kulla-kulla don ganin ya ci gaba da rike jam'iyyar.

Sai dai kuma, kamar yadda wani rahoton The Nation ya bayyana a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, hankalinsa da na masu yi masa biyayya bai kwanta da mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Illiya Damagum ba.

Kara karanta wannan

Shin Tinubu ne? Atiku ya bayyana wanda ya siyarwa hannun jarinsa na $100m a kamfanin Intels

Sabon rikici ya kunno kai a PDP
Yanzu: Sabon Rikici Ya Kunno PDP Yayin da Atiku da Fitaccen Gwamna Suke Neman Iko, Karin Bayani Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku bai da kwarin gwiwa akan Damagum, rahoto

Sun zargi Damagum da biyayya ga yan G-5, karkashin jagorancin ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa yana fuskantar gagarumin adawa a jam’iyyar PDP, Atiku, da wasu jiga-jigan jam’iyyar na bayar da cikakken goyon baya ga shugaban jam’iyyar da aka dakatar, Iyorchia Ayu, domin samun nasarar dawo da shi.

Majiyoyin jam'iyyar sun fada ma The Nation cewa daya daga cikin manyan dalilan da yasa munakisar da ake kullawa Damagum ya ki cimma nasara shine saboda goyon bayan da yake da shi daga wajen Wike, G-5 da wasu mambobin kungiyar gwamnonin PDP karkashin jagorancin gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.

Ana ganin Bala Mohammed zai yi takarar shugaban kasa

An tattaro cewa kungiyar gwamnonin PDP na kokarin saita babbar jam’iyyar adawa, wanda shine zai kawo karshen rikicin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya yi ganawar sirri da Wike kan zaben 2027, rahoto

Bincike ya nuna cewa shugaban kungiyar, Sanata Bala Mohammed, yay i wata ganawa da Wike, wanda shike jagoran G-5 a kwanaki.

Koda dai an yi ganawar cikin sirri ne, rade-radi daga taron ne yasa Wike ya ayyana cewa bai da niyan takarar shugaban kasa a 2027.

Wata majiya ta ce:

"Bala na sha'awar takarar shugaban kasa a 2027 kuma tuni ya fara dinke baraka a PDP da fadin jam'iyyar."

An fadi hanyar da PDP zata kwace mulki

A gefe guda, Legit Hausa ta kawo a baya cewa wani mai sharhi kan al'amuran siyasa, Akinleye Oluwasegun, ya ce "hanya mafi kyau" babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya, PDP, za ta iya kayar da jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 "shi ne ta hanyar haɗaka".

Akinleye ya yi nuni da cewa, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2019 da 2023, ya riga ya yi kira da a yi amfani da haɗaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel