An Bayyana Dalili 1 da Ya Hana Atiku Komawa Dubai da Zama

An Bayyana Dalili 1 da Ya Hana Atiku Komawa Dubai da Zama

  • Alhaji Atiku Abubakar dai ya daɗe yana takara a zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, ko dai a matakin fidda gwani ko na babban zaɓe
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya shafe mafi yawan lokutansa a birnin Dubai na ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)
  • Duk da cewa da yawa daga cikin masu lura da al'amuran siyasa na ganin Atiku mai shekaru 77 ba zai tsaya takara ba a zaɓen 2027, wani sabon rahoto ya nuna cewa tuni ya fara shirin zaɓe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani rahoto da ya fito ya bayyana cewa, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓukan 2019 da 2023, tuni ya mayar da hankali kan 2027.

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana dalilin da ya sanya PDP ta kasa hukunta Wike da yan G-5

A cewar rahoton da jaridar The Nation ta wallafa a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, Atiku ya ƙuduri aniyar cigaba da riƙe madafun ikon jam’iyyar PDP, shiyasa har yanzu ya ƙi komawa Dubai.

Atiku Abubakar bai koma Dubai ba
Atiku ya dade yana takarar shugaban kasa ba tare da nasara ba Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Dubai sanannen birni ne a cikin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin shugabanci a PDP

Jaridar ta ce "wata majiya mai tushe" ta bayyana cewa sansanin Atiku bai ji daɗin Ilya Damagum, shugaban riƙo na jam'iyyar PDP na ƙasa ba, "saboda bin son zuciya na shugabannin PDP irin su Nyesom Wike".

Wike shi ne minista mai ci na babban birnin tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Rivers.

Majiyar wanda ba ya so a bayyana sunansa, ya bayyana cewa:

"Bayan ya sha kaye a zaɓen shugaban kasa da ya gabata, Atiku yana shirya maƙarƙashiyar ɗamke jam’iyyar PDP domin ya sake tsayawa takara a 2027. Har yanzu ya yi imanin cewa yana da sauran dama."

Kara karanta wannan

Magidanci ya maka matarsa a gaban kotu kan aure bisa aure, ya nemi wata bukata 1

"Wannan shi ne babban dalilin da ya sa har yanzu bai koma Dubai da ke UAE ba. Saɓanin ikirarinsa na cewa yana kare dimokuraɗiyya ne a ƙasar nan."
"Tsohon mataimakin shugaban ƙasan da tawagarsa sun fahimci cewa babban koma-bayan da ya samu a zaɓen da ya gabata shi ne bai iya sarrafa jam'iyyar PDP gaba ɗaya ba. Akwai rashin jituwa a cikin jam’iyyar amma ba tare da an yi hukunci ba.

An Bayyana Dalilin Kin Hukunta Wike a PDP

A wani labarin kuma, shugaban riƙo na jam'iyyar PDP ya bayyana dalilin da ya sanya bai hukunta Wike da sauran waɗanda suka ci dunduniyar jam'iyyar ba.

Umar Iliya Damagum ya bayyana cewa ƙoƙarin sasanci yake yi a jam'iyyar kuma idan za a yi hukunci to lallai za a hukunta ƴaƴan jam'iyyar masu yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel