Babban Malamin Addini Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Ga Wike Kan Rikicinsa da Gwamna Fubara

Babban Malamin Addini Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci Ga Wike Kan Rikicinsa da Gwamna Fubara

  • An samu takun saƙa tsakanin Nyesom Wike wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Rivers da kuma Siminalayi Fubara wanda ya gaje shi
  • An yi amanna cewa rikicin na su ya samo asali ne saboda yadda ake tafiyar da harkokin siyasa a jihar ta yankin Kudu maso Kudu
  • Rikicin da ke tsakanin ƴan siyasar biyu ya ƙaru a watan Oktoba, inda ya kai ga yunƙurin tsige Gwamna Fubara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Port Harcourt, jihar Rivers - Fasto Godwin Ikuru, shugaban cocin Jehovah Eye Salvation, ya roƙi Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja da ya ɗagawa yaronsa ƙafa, Siminalayi Fubara, gwamnan jihar Rivers.

Fasto Ikuru, wanda kuma jigo ne a jam’iyyar APC, ya bayar da wannan shawarar ne a wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

PDP ta shiga tangal-tangal yayin da sabuwar rigima ta kunno kai kan rikicin Wike da Fubara

An ba Wike shawara kan rikicinsa da Fubara
Fasto Ikuru ya shawarci Wike ya kyale Gwamna Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Rikicin Rivers: Ikuru ya shawarci Wike

Jihar Rivers ta fada cikin rikicin siyasa tun a ƙarshen watan Oktoba sakamakon yunkurin tsige Gwamna Fubara da wasu ƴan majalisa suka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike wanda tsohon gwamnan Rivers ne, ya yi zargin cewa Fubara na ƙoƙarin ƙwace tsarin jam’iyyar PDP ne a jihar ta yankin Kudu maso Kudu.

Da yake tsokaci kan rikicin, fasto Ikuru ya rubuta a shafin Facebook cewa:

"Wike ka bar yaronka gwamna."

Ayodele ya magantu kan rikicin Wike da Fubara

Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Babatunde Elijah Ayodele ya yi magana kan rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar Rivers a tsakanin Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara.

Babban faston ya bayyana cewa ba lallai ba ne rikicin na manyan ƴan siyasar jam'iyyar PDP a jihar ta Rivers ya zo ƙarshe nan kusa ba kamar yadda wasu ke zato.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da rikicin manoma da makiyaya ya barke a jihar Arewa

Wike Ya Caccaki Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya cacccaki gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, inda ya bayyana shi a matsayin butulu.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya yi nuni da cewa baya son mutane masu butulci yayin da ya zargi Gwamna Fubara da kawo rikici a jihar Rivers.

Asali: Legit.ng

Online view pixel