Watanni 6 da Shiga Ofis, Ana Rade Radin Gwamnan APC Zai Koma Jam’iyyar PDP

Watanni 6 da Shiga Ofis, Ana Rade Radin Gwamnan APC Zai Koma Jam’iyyar PDP

  • Babu jituwa ko na sisin kobo tsakanin masoyan gwamna Hyacinth Allia da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Benuwai
  • Shugabannin APC suna ta samun matsala da sabon gwamnan tun da ya karbi mulki duk da cewa ana jam’iyya guda
  • Wasu sun fara jita-jita cewa Gwamna Allia ya fara yin kus-kus da jagororin PDP domin ya fice daga jam’iyyar APC

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Benue - Rigimar cikin gidan jam’iyyar APC a jihar Benuwai ta kara muni tsakanin mutanen gwamna Hyacinth Alia da abokan fadansu.

Babu jituwa tsakanin magoya bayan Gwamna Hyacinth Alia da shugabannin da ‘yan jam’iyyar APC duk da ana tare a cewar Daily Trust.

Matakin da majalisar dattawa ta dauka na rike kudin kananan hukumomin jihar Benuwai ya taimaka wajen kara hura wutan rikicin.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya yi ganawar sirri da Wike kan zaben 2027, rahoto

Hyacinth Alia
Hyacinth Alia da sauran Gwamnonin APC da PDP Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan APC da fada da Gwamnan Benuwai

Wannan karo rigimar ta fito fili, an daina boye-boye tsakanin ‘yan APC da masoyan gwamna Allia wanda ya shiga ofis a karshen Mayu.

Mai ba gwamnan shawara a wajen karfafa matasa, Mkeenem Moses ya bukaci Austin Agada ya yi murabus daga shugabancin APC.

An yi hakan ne bayan shugabannin APC na duka kananan hukumomi 23 sun nesanta kan su daga kantomomin da gwamna ya nada.

Sabanin ne ya jawo ake maidawa juna martani tsakanin mutanen George Akume wanda shi ne sakataren gwamnati da jama’an gwamna.

Rikicin APC: Allia v Tinubu

A ranar Litinin sai aka ji jam’iyyar APC ta na cewa gwamnatin Benuwai ta shirya zanga-zanga domin bata gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Jaridar ta rahoto Sakataren yada labaran APC a Benuwai, Daniel Ihomun, ya nunawa manema labarai cewa gwamna yana yakar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno PDP yayin da Atiku da fitaccen gwamna suke neman iko, karin bayani

Za a sasanta a APC ko gwamna zai shiga PDP?

Dattawa da manyan jam’iyyar APC sun yi zama a gidan gwamnati a karkashin jagorancin Ameh Ebute, su ka nemi bangarorin su sasanta.

Sanata Barnabas Gemade da kuma General Lawrence Onoja (rtd) sun halarci taron da aka yi, inda aka yi kira ga ‘yan jam'iyyar APC su daina rigima.

Wata majiya ta ce gwamnan ya yi zama da David Mark,Gabriel Suswm da Iyorchia Ayu domin ganin ya sauya-sheka daga APC mai-ci zuwa PDP.

Shawarar Attahiru Jega

Kafin a iya shirya zabuka masu nagarta, Attahiru Jega ya ce akwai gyare-gyaren da ake bukata kamar yadda aka samu labari tun a makon jiya.

Tsohon shugaban na INEC ya hurowa Bola Tinubu wuta a kan wadanda ya ba mukamai a INEC ya kuma bukaci a gyara dokar zabe ta 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel