Magana Ta Kare, Gwamnan PDP Ya Lissafa Mutanen Da Za Su Yanke Makomar Mataimakin Gwamna

Magana Ta Kare, Gwamnan PDP Ya Lissafa Mutanen Da Za Su Yanke Makomar Mataimakin Gwamna

  • A karshe, Gwamna Obaseki ya maida martani kan takarar mataimakin gwamna, Philip Shuaibu a zaben da ke tafe
  • Gwamnan ya bayyana cewa miliyoyin mutane ne zasu yanke wanda zai ɗaga tutar PDP a zaben gwamnan jihar Edo na gaba
  • Godwin Obaseki ya yi wannan furucin ne jim kaɗan bayan ganawa da Gwamna Bala Muhammaed na jihar Bauchi ranar Alhamis

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya kawo karshen shirunsa kan burin mataimakin gwamna, Philip Shuaibu, na shiga takarar zama gwamna a inuwar PDP.

Gwamna Obaseki ya yi magan kan takarar Shaibu.
Gwamna Obaseki Ya Jero Mutanen da Zasu Yanke Makomar Mataimkinsa a Edo Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Daily Trust ta ce Shaibu, wanda ya jima yana takun saka da Gwamna Obaseki, ya ayyana shiga takara a zaben gwamnan Edo mai zuwa, ranar Litinin da ta gabata.

Kara karanta wannan

Wasu hadimai sun yi jabun sa hannun gwamnan APC don sace kuɗi? Gaskiya ta bayyana

Amma da yake jawabi a jihar Bauchi ranar Alhamis, Obaseki ya ce mambobin PDP ne kaɗai za su yanke ko Shuaibu zai zama dan takarar gwamna a inuwar jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya faɗi haka ga yan jarida jim kaɗan bayan fitowa daga ganawar sirri da shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Muhammed.

Shin Gwamna Obaseki zai goyi bayan Shaibu?

Da aka tambaye shi ko zai marawa Shuaibu baya, Obaseki ya ce:

"Ni mutum daya ne daga cikin miliyoyin mambobin jam’iyyar PDP a jihar Edo. Ba na jin kuri'a ta kadai za ta iya ba shi damar zama mai rike da tutar PDP a zaɓe mai zuwa."
"Kamar yadda kowa ya sani alaƙa ta da shi mai kyau ce, yana burin shiga ofishin da nake a yanzu, yana da dama, a matsayinsa na ɗan Najeriya, kundin tsarin mulki ya ba shi dama, babu mai iya hana shi."

Kara karanta wannan

Asalin Abin da Ya Hada Ni Fada da Gwamna Inji Mataimakin Gwamnan Jihar Edo

"Jam'iyya ce za ta yanke hukunci, kuma mambobin PDP ne kawai za su yanke wanda zai rike tutar jam'iyyar mu a zaben gwamna mai zuwa a jihar Edo."

Obaseki ya ce ya ziyarci Bauchi tare da tsohon gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel, domin taya Mohammed murnar nasarar da ya samu a kotun daukaka kara da ke Abuja.

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Ta Yi Sabon Shugaba

A wani rahoton kuma Majalisar dokokokin jihar Nasarawa ta zabi sabon kakakin majalisa da mataimakinsa a zaman ranar Alhamis.

Wannan na zuwa ne ƙasa da awanni 48 bayan kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tsige tsohin kakakin majalisar, Ibrahim Balarebe Abdullahi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel