Kano: Gawuna Ya Bi Sahun Kwankwaso, Ya Bayyana Dalilinsa na Barin ADC
- Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Gawuna, ya sanar da sauya sheka daga jam'iyyar hadakar yan adawa ta ADC
- Nasiru Yusuf Gawuna ya sauya sheka ne kwanaki kadan bayan Sanata Rabiu Musa Kwakwaso ya ice daga hadakar 'yan adawa
- Ya danganta ficewarsa da rikice-rikicen cikin gida da shari’o’i da suka dabaibaye jam’iyyar yayin da ya fice domin neman mafita
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar ADC zuwa NDC.
A cikin wata sanarwa da hadiminsa, Mansur Isa Gawuna, ya fitar, ya bayyana cewa Gawuna ya fice daga ADC ne a ranar Litinin 4 ga watan Mayu na shekarar 2026 tare da dimbin magoya bayansa daga dukkan kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Kara karanta wannan
NDC: Kwankwaso ya mika sakon kar ta kwana gabanin rufe rajistar jam'iyyu a Najeriya

Source: Twitter
Daily Nigerian ta wallafa cewa ganarwar ta ce wannan mataki ya biyo bayan tattaunawa da tuntubar juna da aka yi tsakanin Gawuna da mabiyansa, inda suka yanke shawarar komawa NDC domin ci gaba da fafutukar siyasa a wani sabon tsari.
Nasiru Gawuna ya yi murabus daga ADC
A takardar murabus dinsa, Gawuna ya tabbatar da cewa ya yanke shawarar ficewa daga ADC ne saboda rikice-rikicen cikin gida da kuma yawaitar shari’o’i da suka addabi jam’iyyar.
Ya bayyana cewa wadannan dalilai su ne suka sa shi sauya sheka, wanda a cewarsa ya hana shi gudanar da siyasa cikin gaskiya da kwanciyar hankali.
Ya ce:
“Ni, Nasiru Yusuf Gawuna, ina sanar da ficewa ta daga jam’iyyar ADC nan take. Na dauki wannan mataki ne sakamakon matsalolin shari’a da rikice-rikicen cikin gida da suka addabi jam’iyyar, wanda ya sa ba zan iya ci gaba da zama mamba cikin kyakkyawar niyya ba.”
Gawuna ya gode wa jam'iyyar ADC
Gawuna ya kuma gode wa jam’iyyar ADC bisa damar da ta ba shi a lokacin da yake cikinta, yana mai cewa ba zai manta da hakan ba.

Source: Facebook
Rahotanni sun nuna cewa rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye ADC a wasu jihohi, musamman Kano, sun janyo rabuwar kai tsakanin manyan jam’iyyar, lamarin da ke sa wasu daga cikinsu sauya sheƙa zuwa wasu jam’iyyu.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa wannan sauyi da Gawuna ya yi na iya kara wa jam’iyyar NDC karfi a Kano, musamman idan aka yi la’akari da tasirin da yake da shi a siyasar jihar.
Haka kuma, ficewar tasa na nuni da yadda rikicin cikin gida kan iya raunana jam’iyya, har ta kai ga rasa manyan ‘yan siyasa da magoya baya.
Abdullahi Ganduje ya yi magana kan Gawuna
A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilin da ya sa aka gan shi da shugaban ƙasa a kwanakin baya, inda ya je ya hade da Rabiu Musa Kwankwaso.
Ganduje, wanda shi ne tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya kira shi domin tattauna rikicin siyasar Kano da ta dauki zafi a baya-bayan nan.
Tsohon gwamnan ya kuma yi magana game da sauya shekar tsohon mataimakin, Nasiru Yusuf Gawuna da tasirin hakan a siyasar Kano, ya kuma babu wanda ya yi wa masa laifin komai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

