Ana Shirye Shiryen Gyara a PDP, Za a Kira Taron Zaben Shugabanni 3 a Majalisar NWC

Ana Shirye Shiryen Gyara a PDP, Za a Kira Taron Zaben Shugabanni 3 a Majalisar NWC

  • Nan gaba ake sa ran PDP za ta shirya gangami domin zaben shugabannin da za su cike gibin da aka bari a NWC
  • Jam’iyyar PDP ba ta da shugaba na kasa, sakatare da kuma shugaban mata, don haka wajibi ne a maye gurabensu
  • Dakatar da Iyorchia Ayu a PDP ya jawo ya rasa kujerarsa, shiga takara da mutuwa ne sanadiyyar ragowar gibin

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Jam’iyyar PDP ta soma tsare-tsaren yadda za ayi gyara domin ayi adawa da kyau har a iya tunkarar APC mai mulki.

Majiyoyi daban-daban sun shaidawa Daily Trust PDP za ta kira karamin gangami domin a cike guraben da ake da su a NWC.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban INEC, Jega Ya Soki Hukuncin Zaben Kano, Ya ba Tinubu Shawara

'Yan PDP
Magoya bayan Jam'iyyar PDP Hoto: Official Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria
Asali: Facebook

Taron zai taimakawa jam’iyyar hamayyar wajen shiryawa zabe mai zuwa na 2027 da wuri bayan kunyan da PDP ta sha a bana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mukaman da ake nema a PDP NWC

Yanzu haka akwai gibin mukamai uku a majalisar da ke gudanar da PDP a matakin kasa, don haka za a zabi wasu shugabannin.

Kotu ta cire Dr Iyorchia Ayu daga matsayin shugaban jam’iyya saboda dakatar da shi a Benuwai, dole za a nemi wani sabon shugaba.

A dalilin takarar Samuel Anyanwu, an samu rabuwar kai game da wanda ya dace ya rike kujerar sakataren jam’iyyar PDP na kasa.

Bayan haka akwai kujerar shugabar mata ta jam’iyya da yanzu babu wanda yake kai tun sa'ilin da Farfesa Stella Effah-Attoe ta rasu.

Wa zai zama sabon shugaban jam'iyyar PDP

Rahoton ya ce ana kokarin ganin kujerar shugaban jam’iyya za ta tsaya a yankin Arewa maso tsakiya inda Iyorchia Ayu ya fito.

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: Atoni Janar na Kano Dederi ya shiga matsala, an nemi a hukunta shi

Daga cikin wadanda sunayensu yake yawo akwai tsohon gwamnan jihar Benuwai, Sanata Gabriel Suswam wanda aka tsige a majalisa.

Akwai masu ganin tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ya dace da kujerar, shi ma ya fito daga yankin (jihar Kwara).

Nyesom Wike yana so Saraki ya rike PDP?

Kwanaki aka ga Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ziyarci Bukola Saraki har gida, hakan ya jawo aka fara tunanin akwai shirin da ake yi.

Ana tunanin tsohon gwmanan Ribas ya na cikin wadanda ke goyon bayan Dr. Saraki ya karbi ragamar daga hannun Amb. Iliyasu Damagum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel