Bayan Rasa Mukaminsa, Ministan Tinubu Ya Koma PDP domin Takarar Gwamna
- Tsohon minista a gwamantin Bola Tinubu, Uche Nnaji ya sauya sheka zuwa PDP a ɓoye tare da kokarin neman takarar gwamna a jihar Enugu
- Uche Nnaji, shi ne ministan da aka bankado badakalar da ya yi na karyar kammala digiri har da takardar shaidar yin bautar kasa na NYSC
- Wannan lamari ya raba shi da mukamin ministan kirkire-kirkire da kimiyya da fasaha, sai dai kwatsam aka hango shi zai nemi kujerar gwamna
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Enugu – Tsohon Ministan Kirkire-kirkire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP a boye.
Uche Nnaji ya sauya shekar ba tare da an ji amonsa ba duk da rikicin da ke tattare da zarginsa da badakalar karyar takardun kammala jami'a.

Kara karanta wannan
2027: APC ta kwantar da hankalin Pantami, ta ba shi dama kan batun takarar gwamna a Gombe

Source: Twitter
Premium Times ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa Nnaji, wanda ya tsaya takarar gwamna a jihar Enugu a zaɓen 2023 amma bai yi nasara ba.
Yadda aka zargi tsohon minista da badakala
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Mista Uche Nnaji ya fice daga APC ne bayan ya sauka daga mukaminsa na minista a watan Oktoba na shekarar 2026.
Wannan ya faru ne kwanaki uku kacal bayan wani bincike ya bankado zargin cewa ya ƙirƙiri shaidar digiri daga Jami’ar Najeriya Nsukka (UNN) da kuma takardar shaidar hidimar ƙasa ta NYSC.
Ba tare da sanarwa a kafafen yada labarai ba, Nnaji bai fito fili ya bayyana ficewarsa daga APC ko komawarsa PDP ba.

Source: UGC
Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa yana gudanar da tarukan siyasa da magoya bayansa tare da wasu ‘yan PDP a jihar Enugu.
Sakataren PDP na ƙasa a wani ɓangare na jam’iyyar, Samuel Anyanwu, ya tabbatar cewa tsohon ministan ya shiga jam’iyyar.

Kara karanta wannan
An gudu ba a tsira ba: Guguwa ta tunkaro NDC awanni da sauya sheƙar Kwankwaso da Obi
Duk da haka, mai magana da yawun Nnaji bai mayar da martani ba kan tambayoyi da aka masa dangane da sauya shekar tasa.
Tsohon minista na neman zama gwamna
Duk da cewa yana ƙarƙashin binciken Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), Nnaji na ci gaba da yunƙurin tsayawa takarar gwamna a 2027.
Rahotanni sun nuna cewa ya ƙaddamar da wata ƙungiyar magoya baya mai suna “Uche Ndi Enugu Grassroots Movement” domin tallafa masa.
A cewarsa, idan aka zaɓe shi gwamna, zai yi wa’adin shekara huɗu kacal ba zai nemi lallai sai ya koma kan kujerar ba.
Ya ce:
“Ina son in bayyana a cewa zan yi wa’adin shekara huɗu kacal idan aka zaɓe ni gwamna a 2027.”
Sai dai wannan buri na siyasa yana zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da bincike kan zargin ƙirƙirar takardun karatun bogi.
Rahotanni sun nuna cewa ICPC ta fara bincike tun watan Fabrairu na shekarar 2026 kuma akwai yiwuwar gurfanar da shi a kotu idan aka tabbatar da laifin.
Kungiyoyi sun dura kan tsohon minista
A baya, mun wallafa cewa wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun taso Uche Nnaji a gaba a lokacin da ya ke Ministan kimiyya da fasaha a gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
An rike masa wuta ne a kan zarginsa da amfani da takardun digiri da NYSC na bogi.
Kungiyar GGSMD ta bukaci Ministan ya yi murabus daga mukamin nan take saboda da takardun karya ya yi amfani wajen nadinsa.
Asali: Legit.ng
