Sanatan APC Ya Tsokano Rigima da Ikirarin Babu Aikin da Buhari Ya Yi a Shekara 8

Sanatan APC Ya Tsokano Rigima da Ikirarin Babu Aikin da Buhari Ya Yi a Shekara 8

  • An yi wata hira Jimoh Ibrahim inda ya kare gwamnatin Bola Ahmed Tinubu daga sukar da mutane su ke yi mata
  • Amma kuma Sanatan ya nuna babu wani aikin kirki da za a nuna da Muhammadu Buhari ya yi da yake kan mulki
  • Magoya bayan jam’iyyar APC da masoyan tsohon shugaban kasa Buhari sun yi kaca-kaca da Sanatan jihar Ondo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Jimoh Ibrahim mai wakiltar Kudancin jihar Ondo a majalisar dattawa, ya ce dole ne gwamnatin tarayya ta ci bashin kudi.

A hirarsa da tashar Channels, Sanata Jimoh Ibrahim ya ce ta hanyar karbo aron kudi ne gwamnati za ta iya tafiyar da tattalin arziki.

Sanatan APC
Sanata Jimoh Ibrahim, CFR ya taba Muhammadu Buhari Hoto: @JimohIbrahimCFR
Asali: Twitter

Dole gwamnati ta ci bashi inji Sanata

Kara karanta wannan

Ba za ta yiwu ba: Sojoji sun fusata Pantami da hadimin Buhari da kisan masu Maulidi

Attajirin ‘dan siyasar ya bada misali da UAE mai mutanen da ba su wuce miliyan 12 ba, ya ce ana bin Dubai bashin Dala biliyan 168.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jimoh Ibrahim wanda aka karbewa dukiya a shekarun baya yake cewa gwamnatin Dubai na biyan bashin Dala biliyan 10 duk wata.

Sanatan ya ce babu laifi idan Najeriya mai mutane fiye da miliyan 200, ta karbo aron kudi, ana bin kasar bashin fam Dala biliyan 77.

Ba za a rasa matsaloli ba, amma attajirin mai taurin bashi ya ce sai an ci bashi ne za a iya samar da abubuwan more rayuwa da ke bukata.

A lokacin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ke kokarin gujewa bashi, ‘dan majalisar yana ganin karbo aron kudi ba matsala ba ne.

Akwai makiyan Buhari a APC ne?

Kara karanta wannan

Bani da katabus: Wanda ya kone takardar digirinsa ya yi bayanin dalilansa na bankawa takardunsa wuta

Tolu Ogunlesi ya saurari hirar da aka yi da Sanatan, ya kuma koka a kan yadda yake kokarin ya caccaki gwamnatin Muhammadu Buhari.

Ogunlesi wanda ya yi aiki a matsayin mai ba Buhari shawara yake fada a Twitter cewa Ibrahim ya ce gwamnatin baya ba tayi aiki ba.

A cewar Sanatan na Ondo, babu wani aikin Dala biliyan 1 da Muhammadu Buhari ya yi iya kammalawa har ya bar kan karagar mulki a bana.

Har masoyan APC da ta ba Ibrahim takara sun soki wannan magana, suna ganin akwai wasu ‘yan jam’iyyar da ke kokarin bata Buhari.

The Cable ta rahoto Jimoh Ibrahim yana cewa Muhammadu Buhari ya dawo da abubuwa baya da Goodluck Jonathan ya bar mulki.

Bashir Ahmaad yake fada a Twitter, ya rasa gane manufar wasu ‘yan APC da ke bata gwamnatin baya da alheran da ta yi a shekaru takwas.

Kara karanta wannan

Tinubu ko Buhari: Bulaliyar Majalisa, Ndume, ya bayyana wanda ya fi, ya bai wa kowa maki

Rikicin 'Yan APC da Gwamna a Benuwai

Mai girma Gwamna Hynich Allia yana fada da ‘ya 'yan APC har ana da labari wasu sun fara maganar zai iya tsallaka zuwa jam'iyyar PDP.

Shugabannin jam’iyya mai-ci suna rikici da gwamnan Benuwai saboda rabon mukamai, a cewarsu Allia yana fada da Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel