Babban ‘Dan Siyasa ya Ankarar da Tinubu da Ganduje Wanda Za Ayi Hattara da Shi a APC

Babban ‘Dan Siyasa ya Ankarar da Tinubu da Ganduje Wanda Za Ayi Hattara da Shi a APC

  • Eze Chukwuemeka Eze bai ji dadin hanyar da aka bi wajen sauke shugabannin da ke rike da jam’iyyar APC a Ribas ba
  • ‘Dan siyasar ya ce fifita tsohon gwamnan jihar Ribas a kan Rotimi Amaechi ba daidai ba ne, kuma zai cutar da jam’iyya
  • Duk yadda Nyesom Wike ya yaki jam’iyyar APC a Ribas, Eze ya koka cewa a yau mutanensa Bola Tinubu yake fititawa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Rivers - Wani jagora a jam’iyyar APC, Eze Chukwuemeka Eze, ya yi Allah-wadai da yadda aka ruguza shugabanninsu na reshen jihar Ribas.

Cif Eze Chukwuemeka Eze ya zargi shugabannin APC na kasa da damka jam’iyya a hannun Nyesom Wike, Punch ce ta fitar da wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Jami’an Tsaro sun cika ko ina, NNPP da APC sun hakura da zanga zanga a Kano

Abdullahi Umar Ganduje OFR
Shugaban APC na kasa Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

‘Dan siyasar bai gamsu da matakin da uwar jam’iyya ta dauka na rusa shugabannin APC a Ribas ba, aka nada shugabanni na rikon kwarya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana so a kunyata Amaechi saboda Wike a APC

A jawabin da ya fitar a karshen makon jiya, Eze Chukwuemeka Eze ya ce an yi hakan ne saboda a kunyata Rotimi Chibuike Amaechi a gida.

Eze ya ce shugaban kasa watau Mai girma Bola Tinubu da Abdullahi Umar Ganduje wanda shi ne shugaban APC sun biyewa Nyesom Wike.

Jigon na APC ya yi kira ga jagororin na APC a Najeriya su yi hattara da Nyesom Wike wanda aka ba ministan Abuja, ya ce hawainiya ne shi.

An rahoto ‘dan siyasar ya na gargadin Ganduje da Bola Tinubu cewa tsohon Gwamnan Ribas da aka farantawa rai zai ci amanar APC.

Kara karanta wannan

Wike: Yadda Gwamnan Ribas Ya Tura a Kona Majalisar Dokoki Domin Hana a Tsige Shi

Duk da gwamnatin Wike ta yi kaca-kaca da APC a Ribas tsakanin 2015 da 2023, Eze ya ce an fifita Wike a kan asalin’yan jam’iyyar mai-ci.

"Damka shugabancin jam’iyya ga Wike da mutanensa ba komai ba ne illa mugunta da rashin sanin ya kamata domin tabbas zai kawo matsala.
Sai dai abin takaici ne cewa duk mukaman da Tinubu da gwamnatinsa su ka yi, an fifita Wike ne, wanda ya yaki APC da dukiyar al'ummar Ribas."

- Nyesom Wike

Jam'iyyar APC za ta karbe jihar Kano?

Idan aka koma siyasar Kano, an ji labari Attahiru Jega ya yi Allah-wadai da kataborar da aka yi a shari’ar Abba Kabir Yusuf v Nasiru Gawuna.

Masanin harkar siyasan ya ce akwai sauran aiki gaban hukuma idan ana so ayi zaben kwarai ya kuma nemi a canza jami’an da aka nada a INEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel